Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume na ganawa da ministoci kan zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da matasan Nijeriya ke shirin yi a fadin kasar nan.
Ganawar wadda ministoci sama da 40 suka halarta, na da nufin nemo mafita game da zanga-zangar da ake shirin shiga.
- Za Mu Bai Wa Masu Zanga-zanga Kariya Idan Ta Lumana Ce – Sufeton ‘Yansanda
- Shugaba Tinubu Ya Bukaci ‘yan Nijeriya Da Su Soke Zanga-Zangar Da Suka Shirya
Wasu daga cikin ministocin sun hada da Nyesom Wike (Abuja), Yusuf Tuggar (Al’amuran kasashen waje), Zephaniah Jisalo (Ayyuka na Musamman), Tahir Mamman (Ilimi), da Abubakar Bagudu (Kasafi).
Ragowar su ne Wale Edun (Kudi), Mohammed Idris (Yada Labarai), Bello Matawalle (Karamin Ministan Tsaro), David Umahi (Aiki), da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, da sauransu.
Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata ya roki ‘yan Nijeriya da kada su shinga da zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta, 2024.
Ya zuwa yanzu dai ba san fuskokin wadanda za su jagoranci zanga-zangar ba.
Farashin abinci da kayayyaki na yau da kullum sun na ci gaba da tashin gwauron zabi tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur.
Kazalika, sauye-sauye kan canjin kudaden kasashen waje ya taimaka wajen hauhawar farashin kayayyaki, wanda hakan ya sake jefa miliyoyin ‘yan kasar cikin kangin talauci.