A shekarar 2019 ne, Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin garkame daukacin iyakokin Nijeriya.
Tsohuwar gwamnatin, ta kuma bayar da umarnin haramta shigo da wasu kaya cikin wannan kasa da kuma fitar da su daga cikin kasar, musamman kayan abinci domin a kara habaka harkokin noma a Nijeriya tare da samar da wadataccen abinci a fadin kasa baki-daya.
- Matar Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu 4 A Gusau
- Hadarin Da Ya Auku Ya Bankado Karyar Japan Game Da Ruwan Dagwalon Nukiliyar Da Take Zubarwa A Teku
Barin iyakokin kasar kara zube, shi ne ya jawo tabarwarewar tattalin arzikin Nijeriya shekaru da dama da suka gabata.
Haka zalika, kayan da ake sarrafawa a kasar waje ake shigowa da su cikin Nijeriya, su ne suka tilasata wa masana’antu da dama na cikin gida garkamewa.
Wannan ne ya yi sanadiyyar dubban ma’aikatan da suke aiki a wadannan masana’antu rasa ayyukansu.
Ko shakka babu, wannan al’amari a bayyane yake; musamman idan aka yi la’akari da yadda Arewacin wannan kasa ta yi fice wajen habaka fannin tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ta hanyar aikin noma a Nijeriya.
Har ila yau, karkame iyakokin kasar ya samar da damar samun kara bude masana’antun sarrafa shikafa a Arewacin wannan kasa, wanda hakan ya bayar da damar samun dimbin ayyukan yi a yankin.
Haka zalika, rufe iyakokin ya bai wa ‘Yan Nijeriya da dama rungumar wannan fanni na aikin noma, wanda ya yi sanadiyyar karin samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar.
Misali, daga watan Junairu zuwa na Maris din shekarar 2021, fannin aikin noma ya bayar da gagarumar gudunmawa ga tattalin arzikin Nijeriya, wanda ya kai har kashi 22.35 cikin dari na jumullar tattalin arzikin Nijeriya.
“Rufe iyakokin ya bai wa ‘yan Nijeriya da dama damar rungumar fannin aikin noma, wanda hakan ya sa aka kara samar da wadataccen abinci a daukacin fadin wannan kasa baki-daya.”
Sai dai, wasu ‘Yan Nijeriya da dama, na cike da farin ciki a kan umarnin da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar na sake bude iyakokin Nijeriyan, musamman domin ci gaba da shigo da shinkafa, tumatir da kuma sauran kayayyaki zuwa cikin gida Nijeriya.
Har wa yau, a bangaren manoma musamman wadanda ke Arewacin Nijeriya, wannan umarni na Tinubu zai iya jefa makomar rayuwarsu cikin wani mawuyacin hali.
Kazalika, akasarin mazauna yankin na Arewa wadanda suka dauki sana’ar aikin noma, damina da rani das hi suka dogara.
Sannan, bude iyakokin kasar zai iya kassara kayan da ake sarrafawa a Arewacnin Kasar, wanda akasarin masana’antun ba za su iya yin gasa da kayan da ake sarrafawa a kasashen ketare ba, wanda hakan kuma kai tsaye zai karya farashin kayan amfanin gona na manoman da ke wannan yanki.
“Bugu da kari, sake bude iyakokin wannan kasa, zai kawo wa kayan da ake sarrafa wa a Arewa babban nakasu, musamman ganin cewa, mafi yawancin masana’antun ba za su iya yin gasa da irin kayan da ake sarrafawa a kasashen ketare ba, wanda hakan kuma zai karya farashin kayan amfanin gonan manoman da ke wannan yanki.”
Sai dai, wasu mutane da ke yankin na Arewa ba sa yin la’akari da yadda ake yakar hare-haren ‘yan bindiga ta kowanne bangare, misali’ tun daga fannin ilimin boko, aikin noma da sauran harkokin kasuwanci.
Don haka, yanzu lokaci ya yi da gwamnatin tarayya ta hanyar Babban Bankin Nijeriya (CBN), za ta sake auna fa’ida da kuma rashin fa’idar sake bude iyakon kasar tare da daukar matakin da zai fi zama mai sauki ga ‘yan Nijeriya.