Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana cewa, sake bude sansanin masu yiwa kasa hidima da ke garin Maiduguri bayan shafe shekaru yana rufe, tabbaci ne da ke nuna zaman lafiya ya samu a jihar.Â
Kazalika, Zulum ya sake nuni da cewa, Borno jiha ce ta masu son zuba jari kuma masauki na hada-hadar kasuwanci.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin rantsar da masu yiwa kasa hidima rukunin ‘B’ na shekarar 2023 da aka gudanar a sansanin NYSC na wucin gadi da ke Kwalijin koyon harshen larabci na Mustapha Umar El-Kanemi da ke cikin Maiduguri.
A cewarsa, bisa ikon Allah tare da taimakon dakarun soji da da sauran jami’an tsaro na gwamnati da ‘yan sakai, hakan ya taimaka wa jihar Borno wajen murkushe ayyukan ta’addanci na ‘yan kungiyar Boko Haram da suka juma suna addabar jihar.
Bugu da kari, Zulum ya godawa Allah bisa zuwan da masu yiwa kasar hidima suka yi zuwa cikin jihar.