Dan wasan gab ana kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah yana fatan kungiyar sa ta Liverpool za ta koma kan ganiya, bayan doke Eberton 2-0 a wasan mako na 23 a Premier League a ranar Litinin.
A wasan na hamayya na Mersyside Derby, Liverpool ta fara cin kwallo ta hannun Salah a minti na 36 da fara wasa kuma sabon dan kwallon da ta dauka a Janairu, Cody Gakpo ne ya ci ta biyu na farko da ya zura a raga a Liverpool.
- Canji Kudi: Matakin Da Gwamnonin Arewa Suka Dauka Barazana Ce Ga Dimokuradiyya
- Kasar Sin Ta Fitar Da Bayanan Kimiyya Na Na’urar Chang’e-4
Haka kuma kwallon farko da Salah ya ci a Premier League tun bayan 26 ga Disambar 2023, lokacin da ya ci Aston Billa sannan Liverpool, wadda aka doke ta karo uku a wasa hudu a baya bayan nan a Premier League kafin haduwa da Eberton ta koma ta tara a teburi da maki 32.
Bayan da Liverpool ta buga wasa 21 a Premier ta hau kan Chelsea kenan, ita kuwa kungiyar ta Chelsea ta yi kasa zuwa mataki na 10 bayan ta tashi wasa 1-1 da West Ham United a ranar Asabar din data gabata.
Salah wanda ya yi wasa biyar bai ci kwallo ba kafin ranar Talata ya ce fatan da suke yi shi ne su kare a cikin ‘yan hudun farko a bana, domin su buga Champions League a badi.
Liberpool za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ranar Asabar a Premier League, kwana uku tsakani ta kece raini da Real Madrid a kofin zakarun turai na Champions League.