Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa kashi 5.4 cikin 100 na ‘yan Ni-jeriya da suka kai miliyan 4,792,296 ba su da aikin yi a shekarar 2023.
Idan za a iya tuna dai, hukumar ta NBS a shekarar da ta gabata ta yi amfani da wa-ta sabuwar hanya ta binciken ma’aikata, inda ta ayyana wadanda ke cikin ma’aikata sun kai kashi 15 zuwa sama da haka, akwai kuma wadanda sun zarce haka idan aka fadada bincike.
- Dalilin Da Ya Sa Na Dakatar Da Sanusi A Matsayin Gwamnan CBN – Jonathan
- An Kashe Jagororin ‘Yan Bindiga, Sani Black Da Kachalla Makore A Zamfara
A wata sanarwar manema labarai da aka wallafa a rubu’in farko na 2023 da rubu’in farko na farkon 2024 na sakamakon binciken ma’aikatan Nijeriya, NBS ta ce miliyan 116.6, wanda ke wakiltar kashi 53.8% na yawan al’ummar kasar ne ke cikin shekarun aiki.
Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan sadarwa na hukumar NBS, Sunday. J Ichedi, ya ce mata ne ke da kashi 52 cikin dari na wannan al’umma, yayin da maza ke da kashi 48 cikin dari.
Yayin da aka yi nuni da cewa kashi 76.3 bisa dari kwatankwacin mutane miliyan 88.9 ne suka shiga cikin binciken, ya ce Jihar Bauchi ce ta fi kowacce yawan ja-ma’an da suka shiga wannan bincike da kashi 92.3, yayin da Jihar Ekiti ke da mafi karancin kashi 63.4 bisa dari.
Ya ci gaba da bayyana cewa jimlar yawan shekarun aiki a cikin 2023, mutane mili-yan 84.1 suke yin aiki, miliyan 20.6 daga ciki suna tsakanin shekaru 15 zuwa 24.
Sanarwar ta bayyana cewa, a rubu’in farko na shekarar 2024, yawan marasa ai-kin yi ya karu zuwa kashi 5.3 daga kashi 5.0 a cikin rubu’in farko na 2023, inda yankunan birane ke da kashi 6.0 cikin dari na rashin aikin yi, yayin da yankunan karkara ke da kashi 4.3 bisa dari.
“Yawancin ma’aikata a tsakanin masu shekarun aiki ya ragu zuwa kashi 77.3 a ci-kin rubu’in farko na 2024, daga kashi 79.5 cikin 100 na rubu’in farko na 2023. Yawan mutanen da ba su da aikin yi kai kashi 73.2 cikin 100 a rubu’in farko na 2024. An samu raguwar kashi 2.4 idan aka kwatanta da kashi 75.6 a cikin rubu’in farko na 2023.”
Rahoton ya kara da cewa adadin ma’aikatan da ke aikin albashi ya karu zuwa kashi 16.0 a cikin rubu’in farko na 2024, an samu karuwar kashi 3.3 idan aka kwatanta da kashi 12.7 da aka samu a rubu’in farko na 2023.