Mabiya shafinmu barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa cikin sabuwar shekara. Allah ya sada mu da dukkan alherin dake cikinta.
A yau za mu yi magana ne kan sana’ar hada Sabulun Aloe Bera. Shi dai Aloe Bera na dauke da sinadarai dake kyara fata, ya na rage ko kuma ya batar da nankarwa a jikin mace, yana kuma cire yaushin fata da sauransu.
Sabulun Aloe Bera na inganta fata har ya ba da sakamako na ban mamaki.
Yadda ake hada Sabulun Aloe Bera shi ne:
Da farko dai za ki tanadi Aloe Bera Soap base, Bitamin E Capsule, Roba Mazubi da Cokali
Ga Yadda Za Ku Yi.
Da farko dai za ki tanadi AloeBeranki wanda ya rika, sai ki wanke shi, ki dare shi don cire wannan yaukin da ke cikinsa ki saka shi a roba Mai tsafta. Bayan kin saka a roba ko kwano,sai ki samo blender, ki markada shi, idan ya markadu ya na dawowa fari, sai ki zuba a kwano.
Sannan ki samu Sabulun base din ki ana sayar da shi a shagon sayar da chemicals, da kin ce kina son Sabulun base za su ba ki. Ki yayyanka Sabulun base din cikin kwanon silber.
Ki kunna gas din ki ko gawayi sai ki dora ruwa a tukunya ki sa ruwan daidai yadda idan kika saka kwanon silber din da kika sawa Sabulun base zai shiga.
Idan ruwan ya yi zafi sai ki saka kwanon silber din cikin tukunyan kamar turarawa kenan, sai ki yi ta juya Sabulun zai narke, idan ya narke, sai ki sauke ki saka markadadden Aloe Beran ki ciki.
Idan kin saka ki juya ki dauko bitamin E Capsule din ki, za ki iya samun shi a chemist idan kika ce kina son bitamin E Capsule za a baki sai ki yanka shi sai ki saka ruwan cikin hadin ki, ki kawo Kala ko food colour ki saka a ciki don ya ba da kalar Aloe Bera, ki jujjuya hadin har sai sun hadu
Sai kuma ki samo roba wacce za ta ba ki shape din da kike so, ki goge da mai don Sabulun ya fita da sauki.
Ki shafa Mai a robar, ko ta Ice cream ce sai ki zuba hadinki cikin robar, amma kar ki zuba ta a lokacin da take da zafi sosai saboda kar ta kone miki roba, sai ki bar ta ta sha iska za ki iya barin ta ta kwana daya ko ta wuni.
Daga nan sai ki cire ki mata packaging Mai kyau. Shi Kenan Sabulun ki ta yi hadu sai sayarwa.
Za ki iya tallata abinki a kafofin sada zumuntar zamani (Social media)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp