Assalamualaikum jama’a barkan mu da sake haduwa a wannan shafin mami mai dimbin albarka da amfani ga rayuwar dan’Adam.
In sha Allahu yau za mu yi bayani ne a kan yadda ake hada takalmi samfurin Silifas.
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
- Ekiti: Gwamna Oyebanji Ya Yi Nasara A KotuÂ
Abubuwan Bukata
Kwalin magwaji, Robar hancin takalmi, Roba tik, Roba sol, Igiya,, Zamiya, Gam, Almakashi.
Yadda Za A Hada Kuma
Da farko za ki samu kwalinki wanda za ki fidda surar takalmin da za ki hada,sai ki sami wani takalmin wanda kike kasansa ya zama kamar wanda za ki yi, sai ki dora a kan kwalin nan sannan sai ki bi ki zana da biro. Bayan kin zana sai ki sa almakashi ki yanke daidai Kan biron, sai ki dauki wannan kwalin da kika yanko ki dora a kan roba tik ki kara tisawa da biro sannan sai ki sa almakashi ki yanke in kin tashi za ki fid da kafar dama da kafar hagu sai kuma daukar wannan kwalin ki dora akan roba sol shima ki zana kafar dama da ta hagu.
To yanzu sai ki dauki wannan roba sol din ki auna inchi 2 Ba waya (kafa) 2, sai ki yi alama da biro a daidai tsakiyar takalmin in da zai tashi tsakanin ‘yan yatsun kafa da kuma babbar yatsa ta kafa. Bayan nan sai ki dawo kasan takalmin wajen dunduniya shima ki auna inchi 3 sai ki yi alama,sannan sai ki dan kara gaba kadan ki kara yin wata alamar ki kara matsawa gaba kadan ki yi wata alamar (alama 3 za ai saboda igiyoyin takalmin huda 3 za mu sa a kowacce kafa)
Sai ki dauko igiyoyin takalmin ki auna inchi 8 guda biyu, inchi 14 guda 6, wannan igiyoyi da su za mu yi amfani wajen yin igiyoyin takalmin.
Bayan kin kitsa wannan igiya sai ki kama bakin ki Sanya cikin wannan hudoji da mukai na takalmin.
Sai ki samu san fefa ki goge jikin igiya nan daidai Inda za ki shafa gum sannan sai ki fara kangawa a jikin kafarki dan ki san ko zai yi miki cif-cif dai, akwai bukatar a rage ko a kara tsayin igiyoyin. saboda wata kafar ta fi wata tudu.
To bayan an yi wannan sai a shafa gam a kasan roba sol da kuma roba tik din (Inda bai da zane) da kuma jikin zamiyar ta gaba da baya, sai a jingine a bar shi ya sha iska yadda za a gane ya sha iska shi ne in aka taba da hannu za’a ji ba ya danko sai a dakko su a sa wannan zamiyar a tsakiyarsu wato roba sol da tik din sai na manne.
To bayan an yi wannan sai a samu guduma a dan bubbuga sama sama yadda za su manne sosai. To a nan kuma an gama takalmin sai kawai a dauka a kai wa masu goge takalmi su gogo miki gaba daya zagayen takalmin yadda zai tashi kai daya.
Allah ya ba da sa’a.