Barkan mu da sake saduwa a wannan makon inda za mu yi magana kan kiwo. Kiwo sana’a ce da ake gudanar da ita tun daga gidaje har zuwa ruga da Fulani makiyaya kan yi. Sana’a ce da ba’a gadonta.
Ana kiwata dabboni ko tsuntsaye a gida ta hanyar ciyar da su da sauran abincin da aka ci aka rage ko kuma samar musu da nasu abincin daga kayan gona da dusar abinci, idan kuma tsuntsaye ne kamar irin su kaji, agwagi, tattabaru, talotalo da sauran su, akan sake su suna kewayawa a ciki da wajen gida kamar gida ko kwararo suna tsintar abincin da ya zube a kasa.
Sannan kuma su kan je wurin zubar da shara kamar juji su tono kwari da danginsu a haka suke rayuwa, idan sun hayayyafa zuwa wani lokacin wata bukata ta taso sai a kama a kai su kasuwa don samun abubuwan masarufi.
Ana kiwata abubuwan da suka shafi dabbobi kamar shanu, rakuma, dawaki, jakuna, tumaki da awaki. haka nan ta fannin tsuntsaye ana kiwata kaji, zabi, talo talo, tattabaru da sauran su.
Amfanin kiwo
Kiwo na da matukar amfani sosai ga al’umma, kadan daga ciki su ne:
1. Samar da abinci: kiwo na daya daga cikin hanyoyin samar da abinci. dabbobi kar su shanu da sauran su su kan samar da noma da ake amfani da shi kai tsaye a matsayin abincin.
2. Habaka tattalin arziki: Kiwo na daga cikin hanyoyin samun kudi a kasar Hausa, idan karamar bukata ta taso, Akan kama kananan kiwo kamar su kaji a kai kasuwa nan take a samu kudi, babbar bukata kuma akan kai dabbobi, sannan kiwo shi ne tushen Jima da fawa.
3. Sufuri: Haka nan kiwo na taimakawa wajen harkar sufuri. Allah ya ba da sa’a.