Shugaban kungiyar masu gudanar da harkokin sana’ar safarar dabbobi ta kasa a Legas wadda a kafi saninta da suna ‘Amalgameted’ na shiyar kasuwar sayar da dabbobi dake Alabar Rago a cikin garin Legas Alhaji Aminu Isimaila wanda akafi saninsa da suna Aminu Dan Kanawa ya bayyana cewar sana’ar safarar dabbobi a halin yanzu sai hakuri tare da godiyar Allah.
Shugaban kungiyar ta masu sana’ar safarar dabbobi na shiyar kasuwar Alabar Rago, Aminu Isimaila shi ne ya tabbatar da hakan jim kadan bayan kammala karbar bakuncin wadansu bakin fatake da suka kawo dabbobi a kasuwarsa ta Alabar Rago domin sayar wa kabilu da sauran al’umma masu gudanar da harkokin hada-hadar bikin sallar kirsimeti da murnar shigowar sabuwar shekara dake tafe a nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa, kuma shugaban kungiyar ya bayyana ma JARIDAR LEADASHIP HAUSA a Legas gaskiyar wannan al’amari inda ya cigaba da cewa hakika sana’ar safarar Dabbobi a halin yanzu akwai cigaba kadaran kadahan a cewarsa al,amarin ya zama sai dai hakuri tare da hadawa da godiyar Allah idan akayi la’akari da yadda kasuwar Dabbobi take gudana gabannin kirsimeti a shekarun baya da suka gabata.
Ya cigaba da cewa sakamakon tashin gwauron zabi da farashin manfetur yayi a gida Nijeriya ko bayan Dabbobi kowanne kaya ya samu karin farashin kudi a kasuwannin Nijeriya al’amarin da ya janyo tsadar shatar manyan motocin dakwan kaya daga arewacin Nijeriya zuwa jihohin kudu da yammacin Nijeriya.
Aminu Isimaila ya cigaba da cewa awancan lokacin shekarun baya dasuka gabata suna shatar tirela ta dauko masu Dabbobi daga arewacin Nijeriya shigowa cikin garin Legas a kan kudi Naira dubu dari zuwa dubu dari da wani abu amma yanzu kasan cewar lalacewar hanyoyi sai anyo zagaye kafin shigowa Legas acewarsa sannan Kuma ga tsadar maya mayan da manyan motoci suke amfani dashi da Kuma biyan kudin haraji kala kala a kan hanya dana Gwamnati dama wanda bana Gwamnati ba ga dogarawan hanya.