Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya ƙaddamar da motocin bas guda 107 na sufuri domin saukaka wa al’ummar Kano ta Arewa.
Wannan shiri dai na daga cikin ƙoƙarin Sanatan ke yi inganta harkokin sufuri a yankin mazabar Kano ta Arewa da ma faɗin Jihar Kano.
Za a rarraba motocin bas ɗin ne ga waɗanda za su ci gajiyar tallafin a kan kuɗi kaɗan a ƙarƙashin tsarin haya don mallakarsu.
Waɗanda suka fara cin gajiyar shirin sun haɗa da ƴan ƙungiyar ma’aikatan sufurin mota ta ƙasa (NURTW) daga dukkan ƙananan hukumomin Kano ta Arewa.
- Ana Kokarin Rantsar Da ‘Yan APC 16 A Majalisar Filato Ta Barauniyar Hanya – Gwamnatin Jihar
- Majalisar Dattawa Za Ta Kafa Dokar Kare Hakkin ‘Yan Aikatau A Nijeriya
Ana sa ran wannan tsarin zai inganta fannin sufurin cikin gida da kuma haɓaka tattalin arziki ga ma’aikatan sufurin da iyalansu.
Taron ƙaddamar da motocin bas 107 ɗin ya gudana ne a sabon filin wasa na Bichi da ke garin Bichi, wanda ɗimbin jama’a suka nuna jin daɗinsu kan wannan tsari.
Ga hotunan a ƙasa: