Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa zuwa ƙasar Kamaru.
A wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, Ndume ya gode wa gwamnan bisa alƙawarin tura Sojoji domin kare garin da kuma amincewa da gina asibiti, da rijiyoyi, da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a yankin. Ya ce irin waɗannan matakai za su taimaka wajen dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a.
- Zulum Ya Rabawa Talakawan Dikwa Tallafin Kuɗi Da Abinci
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – Ndume
Sanatan ya kuma roƙi mazauna yankin su ci gaba da zama cikin shiri tare da sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko aiki da ake zargin na ƴan ta’adda ne. Ya ce babu yadda gwamnati ko Sojoji za su iya kawo ƙarshen Boko Haram ko ISWAP idan ba tare da goyon bayan jama’a ba.
Ndume ya bayyana ziyarar gwamnan zuwa garin a matsayin abin ƙarfafa gwuiwa, inda ya nemi a ci gaba da samun haɗin kai tsakanin gwamnati da rundunar Soji da ƴan sa-kai domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp