Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani a ranar Litinin ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya saki dukkan masu zanga-zangar #EndSARS da ake ci gaba da tsarewa.
Sani ya ce, ya kamata Tinubu ya saki wadanda ke tsare a gidan yari sakamakon zanga-zangar #EndSars alfarmar ranar 12 ga watan Yuni.
- Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Sabon Harin Bam Na Kaduna
- NITDA Za Ta Wayar Da Kan Al’umma Kan Sha’anin Tsaro Ta Intanet
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon dan majalisar ya rubuta cewa: “A cikin gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yuni da muka yi shekaru 30 da suka gabata, ina kira ga shugaban kasa da ya saki duk wadanda ake tsare da su a gidan yarin Nijeriya saboda zanga-zangar #EndSARS.”
A shekarar 2020, wasu matasan Nijeriya sun fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da yadda ‘yansandan ke gudanar da ayyukansu.
Zanga-zangar ta haifar da kai hare-hare kan wasu ofisoshin ‘yansanda.
Yayin da aka saki wasu daga cikin masu zanga-zangar, wasu kuma anaSanata Sani Ya Nemi Tinubu Ya Saki Masu Zanga-zanga Da Ke Tsare kyautata zaton har yanzu suna tsare a gidan yari.