Sanatoci uku na jam’iyyar APC sun yi murabus daga jam’iyyar mai mulki tare da sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP da NNPP.
Sanatocin sun hada da Ahmad Babba Kaita, daga Katsina ta Arewa, Lawal Gumau daga Bauchi ta Kudu da kuma Sanata Francis Alimikhena daga Edo ta Arewa.
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
- Bayan Shafe Shekaru 7 Yana Adawa Da Zaben Buhari, Karshe Dai Orubebe Ya Koma APC
Sanarwar murabus din nasu na kunshe ne a cikin wasiku da ko wannen ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya kuma karanta yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Yayin da Kaita da Alimikhena suka sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Gumau, ya koma jam’iyyar NNPP.
Tum bayan kada gangar siyasa, ‘yan siyasa da dama sun shiga sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun saboda wasu dalilai nasu na kashin kansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp