Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shaida cewar a bisa jajircewa, sadaukarwa da kokarin dakarun sojojin Nijeriya, sannu a hankali ana ta bankwana da kalubalen tsaro kuma nan kusa kadan matsalar za ta zama tarihi.
Buhari wanda ke jawabi a lokacin da ya amshi bakwancin suke Fira Ministan Ireland, Micheal Martin a kasar Amurka, kamar yadda kakakinsa, Femi Adesina ya nakalto cikin jawabin Buhari, “A ‘yan watannin da suka gabata, da sabbin dabarun aiki na jami’an tsaron Nijeriya ana samun tagomashi sosai wajen yaki da matsalar tsaro.
- An Nada Sanatan PDP Cikin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS
“Za mu ci gaba da yin aikin hadin guiwa da kasashen duniya wajen amfani da na’urorin zamani domin ganin Nijeriya ta koyi muhimman abubuwan da suka dace.”
Buhari ya fada wa Firaministan cewa, bisa annobar Korona da aka fuskanta a lokutan baya, akwai bukatar kasashen duniya su kara hada karfi da karfe waje guda domin nemo hanyoyin ci gaba, ya yi kwarin guiwar darurrusan da aka koya a lokacin annobar zai taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen maida hankali ta fuskacin tabbatar da zaman lafiya da daurewarsa.
Ya tabbatar wa bakon nasa cewa Nijeriya za ta ci gaba da kyautata alakarta da kasar Ireland musamman a bangaren ilimi, inda ya nuna cewa ‘yan Nijeriya da dama suna karatu da aiki a can kasar don haka kyautata alakar zai kara taimakawa.
Shi kuma Mista Micheal Martin, ya shaida wa shugaban Nijeriya Buhari cewa, Ireland za ta zauna da duba hanyoyin da suka dace wajen kyautatawa da kara dankon zumunci a tsakaninta da Nijeriya.
Ya kuma nuna kwarin guiwarsa na cewa kasar tasa za ta kara fadada alakarta da Nijeriya zuwa fannonin da suka shafi kimiyya, taimaka wa Nijeriya wajen shawo kan matsalolin da suke sashin kiwon lafiya da lamuran tsaro.
Ya kara da cewa tarayyar turai da kasashen duniya yanzu haka ya kamata su sake duba wata hanyar ta daban domin samun hanyoyin samun makamashi tun da yakin Ukraine ya kawo musu cikas ta wannan fannin.
A kuma wata ganawar ta daban da firaministan Greece, Kyriakos Mitsotakis, Buhari ya nemi karin hadin guiwa da Nijeriya a fannonin ilimi, lafiya da tsaro.
Shi kuma a nasa fannin Firaministan ya nemi shugaban kasa Buhari day a samu lokaci wajen ziyartar kasar Greece kafin karewar wa’adin mulkinsa, y ace a shirye suke su fadada hanyoyin alaka tsakanin Nijeriya da kasar don kyautata harkokin da za su taimaki kasashen biyu.