Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sumanusi II, ya gudanar da hawan Sallah, bayan jagorantar Sallar Idi a Masallacin Kofar Mata da ke Jihar Kano.
Ya jagoranci Sallar Idin ne a masallacin Juma’a na Kofar Mata da ke Jihar, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tashi da shi, wanda ya hana gudanarwa a filin Idi.
- Gwamna Dauda Ya Karrama Askarawan Zamfara 20 Da Ke Nuna Bajinta A Yaki Da ‘Yan Bindiga
- Rundunar Sojin Ƙasan Nijeriya,Ta Yi Bikin Yaye Sabbin Sojoji 5,937
Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusif, da sauran manyan jami’an gwamnatin Jihar sun yi Sallar idin ne tare da Sarki Sanusi.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ‘yan msandan Jihar ta fitar da sanarwar haramta hawan Sallah a Jihar sakamakon rikicin masarautar da ake fama da shi.
Matakin da tuni gwamnatin jihar, ta ce hurumin gwamnan jihar ne, ya ayyana ko za a yi hawan sallah ko ba za a yi ba, kasancewarsa lamba daya a bangaren kula da harkokin tsaron jihar.
Shi ma dai Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gudanar da Sallar Idin a karamar fadar Nassarawa kamar yadda ya sanar tun da farko.