Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayar da umarnin sakin fursunoni 104 don yi musu afuwa don bikin sabuwar shekara.
Antoni-Janar kuma Kwamishinan shari’ar jihar, Moyosore Onigbanjo ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
- Hada Rubutu Da Karantarwa Ne Babban Kalubalen Da Nake Fuskanta -Amira Sule
- Jawabin Shugaban Kasar Sin Na Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2023
Ya ce gwamnan jihar, ya sanya hannu kan sakin fursunonin biyo bayan taron tattaunawa da ya yi da masu ruwa da tsaki na jihar.
Yafe wa fursunonin na daga cikin dama da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bai wa gwamnoni na yi wa mai laifi gafara, matukar laifin bai taka kara ya karya ba.
Wannan ya yi daidai da sashe na 212(1) da (2) kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Kwamishinan ya ce kwamitin alfamar na jihar ne suka goya wa gwamnan baya kan lamarin.