• English
  • Business News
Thursday, May 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 hours ago
in Ra'ayi Riga
0
Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A cikin kwanakin baya, an yi ta samun albishir ta fannin nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin.

A ranar 19 ga wata, kamfanin Huawei na kasar Sin ya kaddamar da kamfutar da ke dauke da manhajar sarrafa aikin kamfuta na HarmonyOS da ya kirkira, lamarin da ya alamanta muhimmin ci gaban da kasar Sin ta samu ta fannin kera manhajar sarrafa aikin kamfuta, wanda ya sauya yanayin babakere da kamfanonin Microsoft da Apple suka kafa. Sai kuma kashegari, kamfanin Xiaomi na kasar ta Sin ya sanar da fara samar da sassan na’urorin laturoni na Chips samfurin Xring 01 da ya kirkira, matakin da ya sake nuna babban ci gaban da aka samu a babban yankin kasar Sin ta fannin nazarin sassan na’urorin laturoni na Chips nau’in 3nm.

  • Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya 
  • Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

Al’amuran sun sake nuna gazawar Amurka wajen hana ci gaban ayyukan nazarin kimiyya da fasaha na zamani a kasar Sin, duk da kokarinta na yi wa kasar kafar ungulu.

A cikin ‘yan shekarun baya, Amurka na kallon bunkasar kimiyya da fasaha na kasar Sin a matsayin babbar barazana a gare ta, don haka, take ta kokarin yi wa kasar kafar ungulu tun daga fannin samar da sassan na’urorin laturoni na Chips zuwa na na’urorin samar da su, don neman dakile ci gaban masana’antun samar da kayayyakin zamani na kasar Sin. Ko a makon da ya gabata, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Amurka ta fitar da sanarwa game da sabbin dokokin tsaurara kayyade fitar da sassan na’urorin laturoni na Chips zuwa ketare, inda har ta bayyana amfani da sassan na’urorin laturoni na Chips na Ascend kirar kamfanin Huawei na Sin a matsayin abin da ya keta dokokin.

Ma’aikatar kasuwanci ta Amurka ta bayyana a cikin sanarwar cewa, dalilin kayyade yin amfani da sassan na’urorin laturoni na Chips na Ascend kirar kamfanin Huawei a kasuwannin duniya shi ne, don “kiyaye fifikon kasar Amurka ta fannin nazarin fasahar kirkirarriyar basira ta AI, lamarin da ya bayyana me take nufi da manufarta ta sanya “Amurka a gaba da kome”. Sai dai, don kiyaye karfinta da fifikonta, a maimakon ta inganta aikin kirkire-kirkire da kuma hadin gwiwa da sauran kasashe, sai ta dauki matakai na kashin kai da kariyar ciniki, don dakile ci gaban sauran kasashe a fannin.

Labarai Masu Nasaba

Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

Amma kuma kariyar ciniki ba za ta taimaka ga raya sana’o’i da masana’antu a duniya ba. Idan mun lura, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yadda kasar Amurka ta dauki matakai na kare sana’o’in samar da karafa, a maimakon ya hana raguwar guraben ayyukan samar da karafa, sai ya haifar da karuwar kudaden da sana’o’i masu alaka suka kashe. Haka al’amarin yake ma ta fannin samar da sassan na’urorin laturoni na Chips da fasahohin kirkirarriyar basira, domin rashin yin takara da hadin gwiwa da sauran kasashe ba zai haifar da da mai ido ba, illa koma baya da illoli ga sana’o’i masu alaka.

A bangaren kasar Sin kuma, yadda kasar Amurka ke yi mata kafar ungulu don dakile ci gabanta, ya sa wa kamfanonin kasar kaimin gaggauta kirkire-kirkire, don neman tsayawa da kafafuwansu a fannin kimiyya. Idan ba mu manta ba, a farkon bana, kamfanin DeepSeek mai nazarin fasahar kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar da tsarin R1 da ingancin aikinsa ya kai matsayin na sauran tsarukan AI masu matsayin koli na duniya. Har ma jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta yi sharhin cewa, babban kuskure ne ga Amurka yadda take neman dakile ci gaban kasar Sin. Abubuwan da suka wakana a tarihi sun shaida mana cewa, ci gaban fasahohi su kan samu ne daga rikici da takara da juna, a maimakon zaman walwala. Ita kuma tsohuwar mukaddashiyar mai mataimaka wa sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Susan Thornton, ta yi nuni da cewa, matakan kayyadewa da Amurka ta dauka, a hakika sun yi matukar samar da kuzari ga kasar Sin ta fannin kirkire-kirkire, inda Deepseek ya shaida hakan. Ta ce, “ba zai yiwu Amurka ita kadai ta mallaki fasahar kirkirarriyar basira ba, kamata ya yi gwamnatin Amurka ta yi watsi da kariyar ciniki da ma kiyayya da take wa kasar Sin, kuma ta yi hadin gwiwa da kasar, don samar da alfanu ga dukkanin bil-Adama bisa fasahar kirkirarriyar basira.”

Ma iya cewa, Madam Susan Thornton mai idon basira ce game da bunkasar sana’o’i masu alaka da fasahar kirkirarriyar basira. Lallai kawo tarnaki ga wasu ba ya kara wa mai yin hakan sauri da kuzarin tafiya. Matakan da kasar Amurka ke dauka na neman dakile ci gaban kasar Sin, ba zai haifar da kome ba, illa su sa kasar ta Sin ta kara karfinta da gaggauta ci gabanta. Sabo da kamar yadda a kan ce, sara da sassaka ba ya hana gamji toho.

 

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara

Next Post

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 

Related

Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya
Ra'ayi Riga

Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya

1 day ago
A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka
Ra'ayi Riga

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

1 week ago
Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci
Ra'ayi Riga

Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

1 week ago
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
Ra'ayi Riga

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

2 weeks ago
Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?

2 weeks ago
Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba
Ra'ayi Riga

Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba

2 weeks ago
Next Post
zulum

'Yan Ta'adda Na Amfani Da Sojoji Da 'Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri - Zulum 

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5

‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5

May 21, 2025
Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan

Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan

May 21, 2025
Farar Dabarar Da Tsoffin Masana’antu Ke Yi A Kasar Sin Don Tafiya Da Zamani

Farar Dabarar Da Tsoffin Masana’antu Ke Yi A Kasar Sin Don Tafiya Da Zamani

May 21, 2025
Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 

Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 

May 21, 2025
Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn

Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn

May 21, 2025
Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista

Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista

May 21, 2025
Salon “Kasa Daya Manufa Daya” Ya Dace Da “Ayyuka Goma” Na Hadin Gwiwa Da Afirka

Salon “Kasa Daya Manufa Daya” Ya Dace Da “Ayyuka Goma” Na Hadin Gwiwa Da Afirka

May 21, 2025
Sin Tana Da Karfi Wajen Tinkarar Hadari Da Kalubale A Fannoni Daban Daban

Sin Tana Da Karfi Wajen Tinkarar Hadari Da Kalubale A Fannoni Daban Daban

May 21, 2025
Sabbin Ministoci

Boko Haram: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sansanin Sojoji A Hong Ta Jihar Adamawa

May 21, 2025
Sin Ta Soki Yunkurin Amurka Na Hana Amfani Da Chips Kirar Kasar Sin

Sin Ta Soki Yunkurin Amurka Na Hana Amfani Da Chips Kirar Kasar Sin

May 21, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.