Mai Martaba Sarkin Ingila, Charles na Uku, ya kaddamar da wani shiri na magance rashin aikin yi da samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya.
An bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin daukar ma’aikata na Prince’s Trust International (PTI) ranar Talata a Legas.
- Buhari Zai Halarci Nadin Sarautar Sarki Charles A Landan
- Shugaba Buhari Ya Gana Da Sarki Charles III Na Birtaniya A Landon
An gudanar da bikin baje kolin ne tare da hadin guiwar kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA) da kuma Field of Skills and Dreams (FSD).
Mista Will Straw, babban jami’in gudanarwa na PTI, ya ce karancin ayyukan yi kalubale ne a duniya ba ga Nijeriya kadai ba.
Straw, ya yi nuni da cewa matasan Nijeriya na fuskantar matsalolin kwarewa da ayyukan yi.
“Sama da yaran Nijeriya miliyan 10 ba sa zuwa makaranta.
“Da yawa kuma suna barin makaranta da wuri don su fara neman kuɗi; a cikin waɗanda suka kammala karatunsu da yawa za su iya kammala karatunsu ba tare da samun ƙwarewar da ake buƙata don shiga aiki ba.
Don magance wadannan kalubale, Straw ya ce PTI na da burin dinke barakar da ke akwai ta hanyar mai da hankali kan shirye-shiryen da za su baiwa matasa kwarewa.
Straw ya lura cewa mai martaba Sarki Charles III ya kafa PTI ne domin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa a duniya.
Ya kara da cewa yanzu haka ana gudanar da irin wadannan shirye-shiryen cikin kasashe 23 na duniya.
A cewarsa, PTI tare da haɗin guiwar abokan hulɗa na gida suna aiki tukuru don samar da damarmaki don bunkasa ƙwarewa, sadarwa, juriya da kuma amincewa da matasa don samun nasara da kuma samar da sakamako na aiki.
“Muna aiki tare da abokan hulɗa na gida don isar da ilimi, aikin yi da shirye-shiryen kasuwanci waɗanda ke ba matasa damar koyo, samun kuɗi da bunƙasa rayuwarsu,” in ji shi.
Straw ya ce PTI na hada kai da kamfanoni masu zaman kansu domin daukar matasa aiki, inda ya ce kashi 96 cikin 100 na matasan da suka gudanar da shirye-shiryensu ana daukar su aiki ne cikin watanni uku.
“Burinmu a Nijeriya shi ne samar da damarmaki da zasu canza rayuwar matasa da nufin tallafa wa dubun-dubatar matasa kai tsaye a shekaru masu zuwa,” in ji shi.