Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar 25 ga watan Nuwamba, zai naɗa ɗansa na farko, Aminu Sanusi Lamido, wanda Ɗansanda ne mai mukamin mataimakin Sufurtandan ‘yansanda (DSP), a matsayin Ciroman Kano.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, sarautar Ciroman Kano wani muhimmin mukami ne na al’ada da siyasa a masarautar Kano wanda a al’adance ake bai wa yarima ko mai jiran gado.
Ana bayyana nadin rawanin na Ciroman Kano a matsayin wani muhimmin lamari ga shugabancin masarautar a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp