• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sarkin Musulmi Ya Nuna Baƙin Ciki Kan Kisan Kiyashi A Binuwe

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
Musulmi

Jama’atu Nasril Islam (JNI), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ta bayyana irin baƙin ciki da tashin hankalin da Sarkin Musulmi Ya shiga game da sake samun kisan kiyashi a wasu sassan jihar Binuwe.

A wata sanarwa da Sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, an bayyana cewa Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da wannan mugun aiki, inda ya bayyana kisan gillar a matsayin wanda bai dace da halin ɗan Adam ba kuma ya saɓawa dukkan ƙa’idojin addini.

  • Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji A Sokoto
  • Ya Kuɓuta A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan Shafe Kwanaki 8 Yana Gudu A Dajin Sokoto Da Neja

JNI ta yi tambaya game da dalilin da yasa har yanzu ba a iya kawar da irin wannan tashin hankalin ba, yayin da aka yi kira ga hukumomi da su daina kasancewa masu jiran abin da zai faru kafin su ɗauki matakin kariya. Ƙungiyar ta kuma nuna rashin gamsuwa da yadda jami’an tsaro sukan iso wurin da laifuka suka riga suka faru.

A yayin da JNI ta amince da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi, ta kuma yi kira ga dukkan ɓangarori da su haɗa kai don kawo ƙarshen wannan rikici. Ta buƙaci gwamnati, masu addini, ƙungiyoyin farar hula, da shugabannin al’umma su taka rawar gani wajen hana irin wannan tashin hankali.

“Ya isa! Yin shiru ko kuma rashin kula da lamarin na iya ƙara ƙarfafa wa ƴan ta’add,” in ji sanarwar. JNI ta kuma tunatar da cewa rayukan mutane masu tsarki ne kuma dole ne a kiyaye su bisa dukkan ƙa’idojin addini da na ɗan Adam.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Labarai

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
Labarai

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
Labarai

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Next Post
Ministan Waje: Kwakkwaran Zumunci Da Ake Sadawa Da Sin Ya Yi Tasiri Mai Kyau Ga Al’ummar Rwanda

Ministan Waje: Kwakkwaran Zumunci Da Ake Sadawa Da Sin Ya Yi Tasiri Mai Kyau Ga Al'ummar Rwanda

LABARAI MASU NASABA

Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma

October 24, 2025
An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya

October 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

October 24, 2025
Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.