Shekaru 9 a jere ke nan, WHA, watau dandalin koli na tattaunawa na hukumar lafiya ta duniya (WHO) na kin amincewa da bukatar yankin Taiwan na halartar taronsa.
Idan yankin Taiwan da masu zuga shi ba za su gaji da neman ta da hargitsi ba, to ba za mu gaji da jaddada musu cewa, yunkurinsu na ballewa ba zai taba cimma nasara ba, kuma yankin zai ci gaba da kasancewa wani bangare na kasar Sin da ba zai iya ballewa ba.
- Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Duka Har Lahira A Edo
- Rasha Ta Ce Za Ta Tattauna Da Ukraine Don Yin Sulhu Game Da Yaƙin Da Suke Tafkawa
Manufar kasancewar Sin daya tak kuma halaltacciya mai wakiltar dukkan yankunan kasar, abu ne da daukacin kasashen duniya suka amince da shi, haka kuma kuduri ne mai lamba 2758 da MDD ta zartas, da ya kamata kasa da kasa su yi biyayya gare shi.
Idan Taiwan na ganin tana samun goyon baya daga wata kasa mai karfi, to kasashe 183 a duniya ne suka riga suka kulla huldar diplomasiyya da Sin bisa amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya, don haka, sarkin yawa ya fi sarkin karfi.
Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a duniya ta kowacce fuska, ciki har da tallafi da hadin gwiwa a bangaren lafiya da kasa da kasa, inda ta shafe shekaru sama da 60 tana tura jami’an lafiya da kwararru zuwa kasashen dake fadin duniya. Don haka tabbas Sin tana da iko, kuma ita ta cancanta ta kula da duk wasu harkoki na Taiwan ba wai yankin ya yi gaban kansa wajen nuna shi ’yantacce ne ba. Baya ga haka, kasar Sin tana ba yankin damarmaki ana damawa da shi a harkokin hukumar ta WHO da ma ba shi damar samun bayanai da rahotanni na gaggawa daga hukumar, karkashin manufarta ta “kasa daya mai tsarin mulki 2”. Bugu da kari, kasar Sin ta kasance mai sanya muradun al’ummarta gaba da komai, don haka, ba ta taba barin mutanenta na yankin a baya ba.
A bana ake cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na II da ma dawowar yankin Taiwan karkashin ikon babban yankin kasar Sin, wadda nasara ce da babu wanda zai goyi bayan lalata ta, sai masu neman cimma wani buri na kansu. La’akari da shekarun da aka shafe, da tsayawar kasar Sin tsayin daka kan tabbatar da iko kan yankunanta, ya kamata yankin Taiwan da masu tunzura shi su fahimci cewa, suna bata lokacinsu domin manufar kasar Sin daya tak, manufa ce da ta samu amincewar kasa da kasa kuma babu wanda zai iya sauyata. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp