Sashen aikewa da kunshin sakwanni cikin sauri na kasar Sin, ya samu gagarumin ci gaba cikin watanni bakwai na farkon shekarar bana, inda ya samar da hidimar aikewa da kunshin sakwanni har biliyan 112.05 cikin watannin bakwai na farkon shekarar ta bana, adadin da ya karu da kaso 18.7 bisa dari kan mizanin shekara.
Alkaluman hukumar dake lura da harkokin aikewa da sakwanni ta kasar, sun nuna cewa sashen gidan waya na Sin, ya aike da kunshin sakwanni da suka kai biliyan 122.3 cikin wa’adin na watanni bakwai, adadin da ya karu da kaso 16.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.
Tsakanin watan Janairu zuwa Yulin bana, kudaden shiga daga hada-hadar aikewa da sakwanni na kasar sun kai kusan yuan tiriliyan 1.02, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 142.98, adadin da ya karu da kaso 8.3 bisa dari kan mizanin shekara. A cikin wannan adadi, kudaden shiga a fannin aikewa da kunshin kayayyaki cikin sauri ya kai yuan biliyan 839.42, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari.
Alkaluman sun nuna cewa, cikin wa’adin, yawan sakwannin da aka yi jigilarsu a cikin birni daya sun kai biliyan 9.26, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari a mizanin shekara, yayin da wadanda aka yi jigilarsu daga birni guda zuwa wani na daban, suka kai biliyan 100.43, karuwar da ta kai ta kaso 19.9 bisa dari cikin wa’adin na watanni bakwai. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp