Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya, IPMAN za ta yi taro da matatar mai ta Dangote tsakanin Talata zuwa Laraba domin cimma matsaya kan kudin dakon man daga matatar da ke Lekki a jihar legas.
IPMAN ta bayyana yarjejeniyar da aka shirya yi da matatar man Dangote a matsayin wani muhimmin mataki a kokarin da kungiyar ke yi na saukaka farashin man fetur, ta yadda za ta taimaka wajen samar da isasshen man fetur a fadin kasar.
- NPA Ta Kaddamar Da Shirin Sayar Wa Matatar Man Dangote Danyen Mai
- Ƴansandan Sun Damke Mutane 2 Bisa Zargin Kisan Wata Ƴar Kasuwa
Sakataren yada labarai na kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Arise a jiya Lahadi, inda ya ce, kungiyar na fatan ganawa da jami’an matatar man Dangote domin tattaunawa, cewa, kungiyar a shirye ta ke ta fara kyakkyawar huldar kasuwanci da matatar.
Ukadike ya ce, kungiyar ta samu gonakin tankunan man fetur domin inganta wuraren ajiya, don haka ta magance kalubalen da a baya ya kawo mata cikas wurin gudanar da ayyukanta.
LEADERSHIP ta fahimci cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne, matatar man Dangote ta bukaci kungiyar masu gidajen man fetur ta Nijeriya (PETROAN) da ta sake rubuta bukatar neman dankon mai daga matatar.
PETROAN ta bayyana kwarin gwiwar cewa, farashin man fetur na iya raguwa nan da kwanaki masu zuwa da zarar an fara bai wa duk ‘yan kasuwa mai kai tsaye daga matatar.