Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta dakar da biyan karin albashi na Naira N35,000 da ta yi alkawari tun a watan farko da ta biya sau daya tak, duk kuwa da samun kudin shigar da za ta iya biya.
Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo, shi ne ya yi wannan ikirarin a hirarsa da talabijin din Arise ranar Litinin.
- Shari’ar Kano: Gwamna Yusuf Da Mataimakinsa Sun Halarci Zaman Kotun Koli
- Malam Isa Gusau, Jami’in Yaɗa Labarai Na Gwamna Zulum Ya Rasu
Kungiyar ta ce ta gabatar wa da Shugaban kasa Bola Tinubu ajanda guda 10 a wani mataki na gabatar da bukatunsu ga gwamnatin tarayya.
Osifo ya ce, gwamnatin Nijeriya ta samu kudaden shigan da za su iya biyan bukatun kungiyar amma sakamakon ba ta son biya shi ya sa ta kasa yi har yanzu.
“Idan ka sanya hannun yarjejeniya da wani, sannan ka gano cewa ba zai yiwu maka ka iya aiwatarwa ba, dacewa ya yi ka kira wanda lamarin ya shafa ku zauna domin sake tattaunawa. Amma ba mu tunanin wannan shi ne matsala, kuma ba mu tunanin zai zama damuwa.
“Saboda za ka ga irin kudaden da gwamnati ke rabawa duk wata. Suna da makudan kudaden da za su iya cika alkawuran da suka yi, amma kuma ba su da zimmar yi shi ya sa ake matakin da ake.”
Osifo ya ce, gwamnati ba ta maida hankali kan ajanda gud 10 da TUC ta gabatar mata ba, duk kuwa da cewa dukkkaninsu sun amince da aiwatar da hakan.
Ya ce, “Matakin karshe da muka cimma a yarjejeniyarmu shi ne za a yi abun da ya dace, amma har zuwa yanzu, ga bayanan da muke da su babu abun da aka yi.”
Ya kara da cewa, suna ganin gwamnati ba ta son cika alkawarun da ta dauka musu ne kawai duk da cewa an wuce matakai daban-daban da ya dace a ce an yi abubuwan da suka dace a kai.
A cewarsa, daga cikin ajanda 10 din, akwai muhimman batutuwan da suka shafi matsatsin rayuwa da al’umman Nijeriya ke ciki sakamakon hauhawan farashin kayayyakin masarufi.