Ministan Ma’aikatar Aikin Noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana Gwamnatin Kasar Saudiyya, a matsayin wadda ta nuna sha’awarta na kafa masana’antun kera kayan aikin noma a Nijeriya.
Kyari ya bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta; wato na manhajar X.
- Zai Yi Wahala A Magance Matsalar Tsaro Matukar… – Janar Lagbaja
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Ministan ya sanar da hakan ne, biyo bayan wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki.
A cewar tasa, manufar ita ce; domin a tallafa wa fannin aikin noma na wannan kasa, musamman ta hanyar kafa masana’antar samar da kayan aikin noma na zamani.
Ya bayyana cewa, yankin Nijeriya na tsakiya; ya yi alkwarin sayen tan miliyan 200,000 na jan nama a duk shekara da kuma sayen Waken Soya tan miliyan daya.
A cewar Ministan, hakan zai kara bayar da wata dama wajen karfafa shirin na fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci a fadin kasar.