Ofishin Jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya shirya taron bankwana ga maniyyata ‘yan Nijeriya guda 20 da aka zaɓa domin gudanar da Umarah a ƙarƙashin shirin masarautar ƙasar.
Shirin, wanda Sarki Salman bin Abdulaziz ya ƙaddamar, yana ɗaukar dukkanin nauyin maniyyata daga sassa daban-daban na duniya don ziyartar Makka da Madina.
- Gobara Ta Hallaka Mutum 66 A Otal Mai Hawa 12 A Turkiyya
- Ana Sa Ran Bude Sabon Babin Raya Dangantakar Sin Da Amurka
A wajen taron, Jakadan Saudiyya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya yaba wa ƙoƙarin masarautar wajen tallafa wa Musulmai da tabbatar da cewa ibadarsu ta gudana cikin sauƙi.
Ya bayyana cewa Saudiyya ta kashe dala biliyan 100 wajen faɗaɗa da sabunta Masallatan Harami guda biyu domin karɓar ƙarin maniyyata.
Jakadan ya kuma ja hankalin maniyyata su bi dokokin masarautar don tabbatar da tsaro da jin daɗinsu.
Maniyyatan sun nuna godiyarsu ga Sarki Salman da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman bisa wannan karamci da jajircewarsu wajen hidimta wa addinin Musulunci da wuraren ibada masu tsarki.