Hukumar Saudi Arabia ta musanta batun sanarwar da ta yaɗu kan cewa an sanya dokar hana Takardar izini (visa) ga ‘yan ƙasa ƙasashe 14, ciki har da Nijeriya. Wannan sanarwar ta zargi cewa ƙasashe kamar Egypt, India, Pakistan, Morocco, Tunisia, Yemen, da Algeria sun shiga cikin jerin ƙasashen da za a saka musu takunkumi.
An ambaci ƙasashen Nijeriya, Jordan, Sudan, Iraq, Indonesia, Ethiopia, da Bangladesh a matsayin waɗanda ba za su iya neman sabbin Takardar izini (visa) na kasuwanci ko ziyar Saudi Arabia ba. An bayyana cewa wannan dokar za ta fara aiki daga ranar 13 ga Afrilu. Haka kuma, an ce duk wani ɗan ƙasa daga waɗannan ƙasashen da ke riƙe da visa mai inganci ba zai iya shiga Saudi Arabia ba, sai dai idan yana da visa ta aikin hajj.
- Saudiyya Ta Raba Tan Hamsin Na Dabino A Nijeriya
- Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI
Sai dai, Cibiyar Yawon buɗe idanu ta Saudiyya ta musanta sahihancin wannan sanarwa a lokacin da aka tuntuɓe ta. Ta bayyana cewa sanarwar da hukumomin Saudiyya suka fitar kawai ta shafi jagorancin tafiye-tafiye na aikin Hajji. Cibiyar ta ƙara da cewa wanda ke riƙe da Takardar izini (visa) ta yawon shakatawa ba zai iya zuwa hajj ko zama a Makkah a lokacin da aka kayyade ba.
Takardar izini (visa) ta aikin hajji ta musamman ce don mutanen da suka yi niyya aikin ibadar hajji, kuma tana aiki ne kawai a lokacin tsayawar watan Dhulhajji. Musulmai da suke son ziyarar Saudi Arabia dole su nemi takardar izinin (visa) ta hajj a maimakon ta na yawon shaƙatawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp