Hukumomin Saudiya sun kama tare da tsare mutum 17,615 da suka yi yunkurin yin aikin hajjin ba tare da izini ba.
Jaridar Saudi Gazzet ta ambato shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin bana Janar Muhammad Al Bassami na bayyana haka, inda ya bayyana cewa 9,509 daga cikinsu mutane ne da suka saba ka’idar bizar aiki da ta zaman kasar.
- Na Fi Son ‘Acting’ Na Tausayi A Fim –Salma Gezawa
- Hajj 2023: NAHCON Ta Cancanci Yabo Da Jinjina Ba Kushe Ba – Almakura
Ya ce an kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.
Al-Bassami ya ce hukumomin kasar kuma sun tisa keyar mutum 202,999 da suka yi yunkurin shiga kasar don gudanar da aikin hajjin ba tare da izini ba.
Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin ya kuma yaba wa ‘yansandan kasar bisa jajircewa da ya ce sun yi a lokacin gudanar da wanna gagarumin aiki cikin kwarewar aiki da basira.
Dokokin Saudiyya sun tanadi cewa duk mutumin da ke zaune a kasar, dole ne ya nemi izinin hukumomi idan yana son gudanar da aikin hajji.