Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nada sabbin mataimaka 215, duk da cewa wa’adinsa ya kusa karewa a ‘yan watanni masu zuwa.
Sanarwar nade-naden ta fito ne a hukumance ta wata sanarwa da Sakatariyar gwamnatin jihar, Dr. (Mrs) Folashade Ayoade, ta sanyawa hannu.
Nadin ya kunshi mutane daga dukkan kananan hukumomi 21 da ke cikin jihar Kogi kuma ya fara aiki daga ranar 29 ga watan Satumba, 2023.