Baya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da rukunin kamfanin jaridun LEADERSHIP ya zaba a matsayin gwarzon shekarar 2023 da muka wallafa muku a makon jiya, har ila yau akwai wasu hazikai da suka samu nasarar shiga cikin jerin gwarazan.
Bikin gabatar da lambar karramawa ta LEADERSHIP, na gudana ne a yayin babban taron mika lambar yabo da jawabai na LEADERSHIP, kuma wannan shi ne karo na 16 da jaridar ke gudanarwa. Kan hakan, ana zakulo jajirtattun ‘yan Nijeriya, hazikan ma’aikata, daidaiku, da kamfanonin da suka yi zarra a bangarori daban-daban domin karrama su.
- Wasanni Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Matasa — Gidauniyar Bukola SarakiÂ
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
A wata sanarwar da kamfanin ya fitar dauke da sanya hannun shugaba, Zainab Nda-Isaiah, ta ce, LEADERSHIP, an zabi jaruman ne bisa nuna bajinta da kwazonsu a bangarori daban-daban na rayuwa da hakan ya taimaka wa cigaban rayuwa da kasar baki daya.
LEADERSHIP ta sanar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a matsayin gwarzon dan siyasa na shekara, a lambar yabon ya yi musharaka da sanatar da ke wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan wajen samunta.
Obi ya samu lambar yabon ne saboda zage damtsensa wajen gudanar da harkokin siyasa ta hanyar janyo matasa a jika da kuma sabunta salon yakin zabensa cikin kankanin lokaci da har ya yi tasiri sosai cikin ‘yan takara kuma ya bayar da mamaki da samun tulin kuri’un da ba a taba tsammani ba.
Shi ne ya samu zama na uku cikin ‘yan takarar da suka fito neman shugabancin Nijeriya a 2023 kuma hakan ya zo wa al’umman kasa da mamaki.
Akpoti-Uduaghan ta samu lambar yabon jarumar ‘yar siyasa ne bisa jajircewarta wajen dakile yunkurin kwace mata nasararta da kuma irin tsangwama da ta fuskanta, duk da cewarta mace, ta tashi tsaye ta bi matakan da suka dace wajen kwato wa kanta ‘yancinta.
Bugu kuma da kari a yayin bikin lambar yabon ta 2023, gwamnoni guda hudu na Nijeriya, sun samu nasarar lashe kambon gwarzon gwamna na shekara. Gwamnonin da suka samu wannan nasarar su ne Mohammed Umar Bago na jihar Neja; Dikko Umaru Radda na jihar Katsina; Fr Hyacinth Iornem Alia na jihar Benue; da kuma Oluwaseyi Makinde gwamnan jihar Oyo.
Gwamnonin sun kasance masu kokarin gudanar da shugabanci na kwarai da biya wa al’ummomin jihohinsu bukatunsu.
Gwamna Bago ya samu lambar yabon ne bisa salon mulkinsa, musamman kan yadda ya fara daukan matakin sabunta jiharsa ta hanyar maida Neja sabuta ta fuskancin shimfida ayyuka a birane da karkakara da kuma bunkasa harkokin zuba hannun jari.
Gwamna Radda kuwa ya samu lambar yabon ne sakamakon azamarsa na farfado da martabar jihar musamman kan shirinsa na kyautata harkokin tsaro da inganta hanyoyin samun bayanai na shawo kan matsalolin da suka shafi tsaro.
Shi kuma Makinde ya dale kan kambun ne bisa zuba maguden kulawa kan gudanar da ayyukan bunkasa jihar da hakan ya janyo fadada jihar da budade hanyoyin samun ayyuka ka dumbin mutane a bangarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Gwamna Alia shi kuma ya zama gwarzon gwamna ne bisa irin yadda ya nuna cewa shi shugaba ne da jama’a za su yarda da shi ta hanyar tabbatar da kula da jin dadin jama’ansa, toshe kafofin sata da yaki da rashawa da almubazzaranci da dukiyar al’ummar jihar Benue.
A wani bari na gwarazan, jaridar LEADERSHIP ta zabi ministan kula da harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo a matsayin gwarzon ma’aikacin gwamnati na shekara, saboda maida hankalinsa wajen kawo gyare-gyara da dakile matsalolin da suke makale a harkokin fasfot a hukumar kula da shige da fice ta kasa. Ita ma manajan gudanarwa na hukumar kula da lamuran sufuri ta jihar Legas (LAMATA), Injiniya Mrs Abimbola Akinnajo ta samu irin wannan lambar yabon na ma’aikaciyar gwamnati mafi kwazo bisa gagarumin jagoranci na kwarai da take yi da kokarinta da ya kai ga samar da layin dogo ‘Lagos Blue Rail line’, shekaru 40 da awatar da shi.
Shugaban rukunin kamfanonin Gerewa, Alhaji Isa Mohammed Gerewa shi ne ya samu lambar yabon gwarzon dan kasuwa na shekara bisa gina kamfanin da ya samu nasara da ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.
Lambar yabon babban jami’in gudanarwa (CEO) kuwa, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Emzor Pharmaceutical Company, Dr Stella Chinyelu Okoli; CEO na otel din Transcorp, Dupe Olusola, da kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Marbelous Mike Press, Engr Micheal Bayo Akinola su ne suka lashe kambon gwarzon jarumin CEO na shekara.
Gwarzon ma’aikaciyar banki na shekara kuwa ya tafi ne kan manajan gudanarwa na bankin FCMB, Mrs. Yemisi Edun, a bisa yunkurinta na hadaka samar da rance ga kananan ‘yan kasuwa da jan ragamar bankin zuwa matakin tallafa wa SME. Yayin da kuma bankin UBA ta samu lambar yabon banki mafi kwazo na shekara bisa gudanar da shirye-shirye masu yawa da suka taimaki kwastomominsu kai tsaye.
Lambar yabon na LEADERSHI bai tsaya haka ba, inda mai martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, CFR, ya samu lambar yabon gwarzon da ya fi damuwa da harkokin zamantakewa da ya fi damuwa da al’ummarsa wanda hakan ya kai ga gagarumin nasarar kyautata harkokin tsaro da bunkasa zaman lafiya a masarautarsa da ma jihar Bauchi baki daya.
Hukumar (FCCPC) ita ce ta samu kambun gwarzon hukumar gwamnati bisa nuna gaskiya, gudanar da ayyuka bisa ka’ida da kuma kare kwastomomi.
Sauran wadanda suka lashe lambar yabon, jarumar kamfani ta shekara ia ce kamfanin Zeberced Group bisa fitar da nagartattun kayayyaki da inganta aiki na kwarai; kamfanin mai da iskar gas na shekara kuwa ita ce kamfanin Seplat Energy Plc; da kamfanin da ke fitar da gas da iskar gas na cikin gida kuwa ita ce kamfanin, Aradel Holdings Plc; IT kamfani kuwa ita ce CWG Plc, sauran kamfanonin da suka samu lambar yabon sun hada da Flour Mills Nigeria Plc da Monie Point.
Gwarzon jarumar shekara kuwa ya tafi ne kan Nike Okundaye Dabies bisa kokarinta na bunkasawa da karfafa mata da matasa kan harkokin zane-zane da fasaha.
A bangaren Gwarzon Wasanni kuwa, tawagar ‘yan was an kwallon Kwando ta Nijeriya D’Tigress ta lashe bisa daga kofin gasar Afro Basket har sau hudu a jere wanda hakan ya kafa tarihi; yayin da kuma Awwalu Sani, wanda ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta na wani dan kasar Chadi da ya mance a cikin keke-napep dinsa shi ne ya samu lambar jarumin matashi na shekara na jaridar LEADERSHIP bisa nuna gaskiya da adalci na mayar da kudin da ya tsinta wanda hakan ya zama abun misali ga matasa da dama.
Dukkanin wadanda suka samu lambar yabon za a mika musu kambun nasu ne a yayin babban taron LEADERSHIP na shekara-shekara da zai gudana a farkon zangon shekara mai zuwa, kuma hukumar gudanarwar jaridar za ta sanar da rana nan kusa.
Tsarin zabin wadanda za su amshi lambar yabon ya gudana ne a watan Nuwamba wanda mahukuntan manya-manyan jagororin (majalisar editoci) na jaridar da sashin kasuwanci hade da manbobin hukumar bada shawarori wadanda kwararru ne a bangarori daban-daban suka cimma.