“Taruka 2”, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, na wannan shekara na karatowa, wadanda suke da muhimmanci matuka, kana wata muhimmiyar hanya ce da jama’ar kasar ke bi, don tsoma baki cikin harkokin siyasa na kasar.
Idan aka nazarci yadda aka gudanar da tarukan 2 cikin shekaru 10 da suka wuce, za a ga yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci tattaunawa da wasu wakilan jama’a ko kuma ‘yan majalisa suka yi, har sau 53, don sauraron ra’ayoyinsu dangane da dabarun raya kasa. Wannan batu ya shaida gaskiyar tsarin dimokuradiya na kasar Sin, da tunanin shugaban kasar na kokarin bautawa jama’a. (Bello Wang)