Tun daga watan Nuwamban 2023 har zuwa Mayun 2024, duk wanda yake bibiyar manyan tarurruka da suka jibanci fafutukar neman mafita a kan matsalolin da suka addabi al’umma musamman ta fuskar shugabanci a Nijeriya, ya san yadda tsohon shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ke yekuwar lokaci ya yi da kasashen Afirka za su dawo cikin hayyacinsu, su sama wa kansu tsarin dimokuradiyya mafi dacewa da al’ummominsu.
Obasanjo wanda ake wa kallon masoyin dimokuradiyya tun yana kakin soja bisa yadda ya cika alkawarin dawo da mulki hannun farar hula kamar yadda marigayi Janar Murtala ya kudiri aniyar yi a shekarar 1979, ya ce tabbas dimokuradiyyar Turawan yamma da Afirka ta dauko ba ta kai nahiyar tudun mun tsira ba kuma dama tilasta mana aka yi mu yi aiki da ita daga ‘yan mulkin mallaka, saboda haka ya kamata mu yada kwallon mangwaro mu huta da kuda.
- Fahimtar Nasarorin Siyasar Jam’iyyar Da Ta Yi Shekaru Dari Da Uku
- Yadda Gidan Buhari Ya Zama Fadar Ziyarar Jiga-jigan ‘Yan Siyasa
“Dimokuradiyyar Turawan yamma ba ta la’akari da abin da mafi rinjayen al’umma ke so. Tana kafa gwamnati ce ta ‘yan tsiraru a kan jama’a wadanda suke aiki domin ‘yan tsirarun nan ba al’umma gaba daya ba,” don haka ya ba da shawarar a fito da tsarin dimokuradiyya da zai dace da yanayi da tarihi da al’adunmu na Afirka domin mai daki shi ya san wurin da yake masa yoyo.
Duk da cewa, wasu za su ce me ya sa Obasanjon bai yi wannan maganar ba lokacin da ya ci gajiyar dimokuradiyyar a wa’adin mulkinsa daga 1999 zuwa 2007? To, amma ya kamata mu lura cewa, idan dattijo irin Obasanjo ko ma wanda bai kai shi ba ya yi magana, a dubi maganar tukuna da farko a dora ta a sikeli, ta gaskiya ce ko akasinta, sannan mai yiwuwa lokacin da aka samu ilhamar maganar ke nan kuma idan aka yi amfani da ita ba a makara ba.
Turawan yamma sun gama shuka mana lalata tun kafin faduwar katangar Berlin a shekarar 1989, lokacin da suka fito da yekuwar ‘kyakkyawan shugabanci’ na fatar baki a matsayin dabarun ci gaba. A cikin shahararriyar kasidarsa “The End of History”, masanin siyasar Amurka, Francis Fukuyama, ya yi shelar cewa karshen yakin cacar baki shi ne “karshen juyin akidar dan adam da kuma fara samun daukakar dimokuradiyyar yamma mai sassaucin ra’ayi a duniya a matsayin tsarin shugabancin dan adam na karshe.”
Irin wadannan kalamai sun yi nuni da shirye-shiryensu na yin tir da duk wata akida da ta saba wa tasu, don haka ba abin mamaki ba ne, yadda tun a shekarun 1990, bankin duniya ne ya zama mai shata wa Afirka abin da ake nufi da shugabanci na-gari da kuma hanyoyin magance dukkan kalubalen ci gaban da kasashen Afirka ke fuskanta. Wannan ya sa har yanzu duk da muna karni na 21, amma muna dandana kudarmu saboda rashin muhimman abubuwan more rayuwa.
Afirka, mun gaji tsarin dimokuradiyya mafi dacewa da al’ummarmu tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Misali, a kasar Hausa, sarakuna kan yi nade-naden sarauta daga sassa daban-daban na kasar da suke mulka kamar hakimai, dagatai, masu unguwanni, domin tabbatar da cewa mutanen kowane yanki suna da wakilci a zaman fada da ake yanke hukunce-hukuncen da suka shafi rayuwar al’umma.
Idan kuma a bangaren bai wa mata ‘yanci ne, an san tarihin Sarauniya Daurama (da ake wa take da uwar Hausa Bakwai), ga Sarauniya Amina a Zazzau. Duk wadannan an yi su ne tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka da shekaru masu yawa.
Dimokuradiyya irin ta yamma kuwa ta kasance ta tauye mutane tun fil’azal, kamar yadda wani marubuci, Damola Adejumo-Ayibiowu ya ce a wata makala da ya rubuta aka wallafa a shafin Open Democracy, a shekarar 2019, “Hasali ma, ba a ba wa matan Birtaniya damar kada kuri’a ba sai a shekarar 1928 a lokacin da yawancin matan Afirka, musamman Yarbawa na yammacin Afirka, ke shiga wajen yanke shawara a dama da su a bainar jama’a ba tare da tauye musu hakki ba.”
“Mafi yawan mulkin dimokuradiyya na Yammacin Turai tsari ne na danniya a fakaice cikin al’ummomin da suka zama ‘yan tsiraru. Amma a cikin al’ummomin Afirka kafin mulkin mallaka irin su Igbo, Yarbawa, da Ashanti na Ghana, ana yanke shawara ne yawanci bisa rinjaye (ijma’i), wanda ketabbatar da cewa an wakilci kowane bangare ta hanyar maslaha domin rage husuma a tsakanin mutane. Abu mafi mahimmanci shi ne, dimokuradiyyar da aka gada daga al’adun Afirka an kafa ce a kan falsafar Afirka ta zamantakewa da kyawawan dabi’unsu. Dimokuradiyya irin ta yammacin duniya kuwa ta samo asali ce daga fafutukar neman ‘yancin kai na magabatanmu wanda aiwatar da ita ta yi illa ga rayuwar talakawa a Afirka.”
Tabbas haka ne, shi ya sa mun kwashe shekaru masu yawa da sunan mulkin ‘yancin kai amma har yau miliyoyin mutanenmu suna fama da kangin talauci sakamakon tsarin shugabancin da aka yaudare mu da shi, baya ga rashin wadatattun ababen more rayuwa.
Amma kuma lokaci bai kure mana ba idan har Afirka za mu farka mu dauki turbar dimokuradiyyar da za ta fi zama mana alheri. Akwai darasin da za mu iya koya daga kasar Sin wadda a shekarar 2007 ne shawarar aiki da “cikakken tsarin dimokuradiyya na bai wa kowa hakkinsa” ya shiga ka’idar siyasar kasar Sin, kuma a yayin babban zaman taro karo na shida na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) karo na 19 a watan Nuwamban shekarar 2021, aka karfafa manufar. Bayan wata guda kacal, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da bayanai a kan matakin da aka amince da shi a hukumance mai taken “Sin: Dimokuradiyyar da za ta biya bukata.”
Hakika matukar muna so mu yada kwallon mangwaro mu huta da kuda, wajibi ne shugabanni masu kishin al’umma su amsa irin kiraye-kirayen da su Obasanjo suke yi na kawo tsarin domokuradiyya mafi dacewa da mu a Afirka wanda zai kawo mana sakamakon da kowa zai shaida a fili.
Irin dimokuradiyyar da za ta fifita muradun mutane a kan na kashin kai ko biyan bukatun siyasa, wadda za ta dawo da mu turbar asali ta ci gaban mafi rinjayen mutane ba ‘yan tsiraru ba. Irin wadda za ta fifita cika alkawari ba magana da fatar baki ba.
Za mu iya ganin misalin haka daga dimokuradiyya ta hakika ta kasar Sin wadda ta fitar da mutane miliyan 770 daga kangin talauci a cikin shekaru 40 da suka gabata, tare da kawar da matsanancin talauci baki daya. Ta tabbatar da kiwon lafiya mai inganci da karfin iko ga kusan kashi 20 cikin 100 na al’ummar duniya, kuma ta yi hakan ne a daidai lokacin da wasu suke ganin dimokuradiyyar dake akidarsu ta afka cikin rudani, gazawar shugabanci, tabarbarewar tattalin arziki da karuwar rashin daidaito tare da nau’o’in rikice-rikice na cikin gida da na duniya da ba su yi kama na a zo a gani ba da dimokuradiyya kwata-kwata.
Muna bukatar dimokuradiyyar da za ta kawo mana cin gajiyar juna kamar yadda muke gani a shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kasar Sin ba ta raba kawuna da hada gaba da kakaba takunkumai a tsakanin kasashe kamar yadda Amurka ke yi ba.