Sama da karni guda ke nan, Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ta hada kan Sinawa wajen raya kasa bisa tsarin gurguzu daidai da dabi’un Sinawa. Manufar jam’iyyar ita ce tabbatar da farin cikin jama’a, da sake farfado da al’ummar kasar, kuma ta samu sakamako na hakika na asali bisa kyawawan manufofin raya kasa. Baya ga nasarorin da suka fi shahara a fannin tattalin arziki da zamantakewa, nasarorin siyasa da jam’iyyar ta samu suna da ban mamaki.
A ko da yaushe JKS tana bunkasa tsarin siyasar kasar Sin bisa tarihin kasar da yanayin kasa, da tabbatar da ingantacciyar alkiblar ci gaban kasa tare da daidaita bukatun tsarin mulkin kasar bai daya. Tsarin dimokuradiyyar Sin ya kasance tamkar tsintsiya madaurinki daya, hakan ya samo asali ne daga hadewar tsarin da aka shigo da shi daga kasashen waje da kuma salon siyasa ta kasar Sin ta cikin gida, wanda ke ba da damar saukaka yanke shawara mai inganci da ake bukata don ci gaban kasa, tare da tabbatar da hadin kan jam’iyya da dimokuradiyyar zamantakewa.
- Masana’antar Kera Bayanan Kayayyakin Laturoni Ta Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Bunkasuwa Daga Janairu Zuwa Mayu
- Kasar Sin Ta Amince Da Dokar Ba Da Agajin Gaggawa Da Aka Yi Wa Kwaskwarima
Tsarin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wanda shi ne tsarin gudanarwa mai matakai daban-daban dauke da tsarin dokoki, ya dace da tsarin kasar a matsayin kasa mai girma da yawan jama’a, da tabbatar da cewa ikon gwamnati na hannun jama’a. Yayin da taron ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin, wanda shi ne mafi kololuwar hukumar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ga gwamnati, ta kunshi daidaituwa a cikin mabambantan yanayi, wanda ke da tushe mai zurfi a cikin al’adun tarihi da al’adun kasar Sin, da tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba. Duk wadannan hukumomi suna nuna hikima da hangen nesa na JKS wajen tafiyar da mulkin kasar.
Jama’a su ne ginshikin kasa, kuma kasa za ta samu zaman lafiya idan har ginshikinta ta karfafa. Hidimtawa jama’a da zuciya daya shi ne ainihin manufar JKS, yayin da take dagewa kan mutunta ra’ayin jama’a, da kiyaye hakki da moriyar jama’a, da kyautata jin dadin jama’a a harkokin siyasar kasar Sin. Wannan falsafa ita ce ginshikin da ta rike jam’iyyar sama da karni guda ba tare da tangarda ba. (Yahaya)