A yanza haka sanatoci biyu kacal ya rage wa jamƴyar APC ta samu kashi biyu cikin uku na yawan ƴan majalisar dattawa, sakamakon sauya sheƙa da sanatoci guda huɗu suka yi daga PɗP zuwa APC a ranar Laraba da ta gabata.
Bisa tsarin kundin mulkin Nijeriya da dokokin majalisar ƙasa, wannan na nufin cewa idan APC ta samu kashi biyu bisa uku na yawan mambobi a majalisar dattawa, kowanne ƙudirin doka ko wata buƙata da aka kawo zauren majalisar dattawa dole sai ya samu goyon bayan APC kafin a amince da shi ko ba tare da goyon bayan ƴan adawar ba.
Masana sharhi kan harkokin siyasa su yi gargaɗin cewa irin wannan rinjaye na haifar da babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya da ke tasowa kuma yana iya haifar da mulkin kama-karya.
- Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
- Wasu Gwamnonin PDP Sun Kulla Makirci Kan Samun Shugaban Kasa Daga Yankin Kudu —Wike
Sanatocin guda hudu da suka sauya sheƙa a makon da ya gabata sun kasance biyu daga Jihar Akwa Ibom da kuma daga Jihar Osun, sun bayyana ficewarsu a lokacin taron zaman majalisar. Sanatocin sun hada da Sanata Sampson Ekong, mai wakiltar Akwa Ibom ta kudu da Aniekan Bassey, mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso gabas da Francis Fadahunsi, mai wakiltar Osun ta gabas da kuma Olubiyi Fadeyi, mai wakiltar Osun ta tsakiya.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta wasiƙar sauya sheƙar a zauren majalisar.
Saboda haka, ƙarfin APC a zauren majalisar dattawa mai mambobi 109 ya kai 70, kujeru biyu kadai take buƙata ta cika 72 don samun rinjaye na kashi biyu cikin uku.
PɗP yanzu haka tana da kujeru 28, yayin da jam’iyyar LP ke da biyar. Jam’iyyar SɗP na da kujeru biyu, yayin da jam’iyyar NNPP da APGA ke da kujeru guda daya kowannansu.
A yanzu haka, akwai kujeru biyu na majalisar dattawa da babu kowa. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), har yanzu ba ta gudanar da zaɓen cire gurbin Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar Anambra ta kudu, wanda ya rasu a farkon wannan shekara, da Sanata Monday Okpebholo, mai wakiltar Edo ta tsakiyar, wanda ya bar kujerarsa bayan lashe zaɓen gwamna na Jihar Edo a 2024.
Kazalika, a majalisar wakilai ma an samu sauya sheƙar mambobi guda uku daga PɗP zuwa APC a ranar Laraba, wanda ya kuma ƙara ƙarfafa ƙarfin jam’iya mai mulki zuwa samun kujeru 224 a cikin kujeru 360 na majalisar. ƴan majalisar wakilan da suka saura sheƙa sun hada da Taofeek Ajilesoro da Omirin Emmanuel Olusanya daga Jihar Osun, tare da Marcus Onobun daga Jihar Edo da kuma Mark Esset daga Akwa Ibom.
Bisa wannan lamari, PɗP yanzu tana da kujeru 86, yayin da jam’iyyar LP take da kujeru 26, NNPP ta da 16, APGA ta da shida, SɗP ta da biyu, sannan ADC tana da daya.
A halin yanzu, akwai kujeru biyar a majalisar wakilai da babu kowa sakamakon mutuwar ƴan majalisar guda huɗu da kuma daya da ya yi murabus.
da yake tsokaci kan samun rinjayen APC a zauren a majalisun tarayya a gaban zabɓen 2027, masana kimiyyar siyasa, Farfesa Gbade Ojo, ya yi gargaɗi game da mummunan sakamako ga makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ya ce, “Abin da muke shaida shi ne, APC na ƙara samun gagarumin rinjaye. ɗuk da cewa hakan na iya bayyana matsayin siyasa mai ƙarfi a zahiri, tasirin wannan ga dimokuraɗiyya yana da matukar damuwa.
“Lokacin da wata jam’iyyar mai mulki a cikin dimokuraɗiyya ta mamaye majalisa har ta samu kashi biyu cikin uku na yawan mambobi, hakan yana zama wani siffofi na mulkin kama-kurya, domin ba za a samu ingantaccen kulawa da daidaito ba,” in ji shi.
Ya ba da shawara cewa a irin wannan yanayi, majalisun tarayya na iya rasa ƴancin kai da zama ƴan amshin shata ga ɓangaren zantarwa.
Ya gargaɗin cewa in har ƴan adwa ba su sake tsarawa ba ta hanyar dawo da tsaftataccen tsarin cikin gida da kafa wani takamaiman aƙidar tunani, dimokuraɗiyyar Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa cikin hatsari da rashin daidaito.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp