Manyan jam’iyyun siyasa a Nijeriya na neman tilasta wa ‘yan majalisa na jihohi da na tarayya wajen kirkiro dokoki da za su ayyana kujerun ‘yan majalisan da suka sauya sheka bayan an zabe su a matsayin babu kowa.
Jam’iyyun sun hada da APC, PDP, LP da kuma YPP dukkansu sun yi barazanar kai karar ‘yan majalisan jihohi da na tarayya kan kawo sauyi na wannan lamari.
- Karancin Wuta: Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Bai Wa AEDC Makonni 2 Don Gyara Wutar Lantarki
- Ranar Ma’aikata: Bayan Cike Giɓin Albashin Da Muka Gada, Za Mu Ci Gaba Da Inganta Walwalar Ma’aikata – Gwamnan Zamfara
Jihohin da aka samu sauya sheka na ‘yan majalisa tunn lokacin da aka rantsar da su sun hada da Anambra, Kogi, Inugu, Ribas, Yobe da kuma Kaduna, sai dai lamarin sauya sheka ya fi kamari a jam’iyyar PDP.
A zuwa yanzu dai, dan majalisar tarayya guda daya ne kacal, Sanata Ifeanyi Uba ya sauka sheka daga jam’iyyar YPP zuwa APC.
A Jihar Yobe kuwa, Hon Lawan Musa Majakura shi ne kadai dan majalisar PDP da ya sauya sheka a zauren majalisar Jihar Yobe a 2023, wanda ya ba shi damar zama shugaban majalisar jihar ba tare da wata hamayya ba.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Yagba ta yamma a majalisar Jihar Kogi, Idowu Ibikunle,wanda aka zaba a jam’iyyar ADP, amma daga baya ya sauya sheka ya koma APC.
A Jihar Kaduna kuwa, Godfrey Ali Gaiya da ke wakiltar Zango Kataf a zauren majalisar jihar ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.
Bisa ga kundin tsarin mulki sashi na 109 (g) ya bayyana cewa, dan majalisa yana iya asarar kujerarsa idan har ya kasance ya sauya sheka daga jam’iyyar da aka zabe shi ya koma wata jam’iyya kafin karewar wa’adin majalisa. Idan kuma ya samu wasika daga jam’iyyarsa sakamakon yin maja na hadewar jam’iiyu biyu ko wani bangare, to babu komi a kansa.
Sauya shekan ‘yan majalisan jihohi na iya hana jam’iyyun lashe wasu mukamai kamar kujerun tarayya, ofishin gwamna ko ma na shugaban kasa.
‘Yan majalisan suna sauya shekan ne domin samun damar yin nasara a zabe mai zuwa, mafi yawancin jami’an jam’iyyu a jihohi suna fadi zabe a hannun abokan hamayya kan wannan matsala.
A cewar wasu jami’an jam’iyyu da suka tattauna da LEADERSHIP sun bukaci kotun kolli ta ayyana kujerun ‘yan majalisan da suka sauya sheka a matsayin wanda babu kowa.
Shugaban jam’iyyar LP a Jihar Inugu, Barrister Casmir Agbo ya ce za su garzaya kotu kan shugaban majalisar jihar ya ayyna kujerun ‘yan majalisa shida da aka zaba a karkashin jam’iyyar LP suka sauya sheka zuwa PDP a matsayin wadanda babu kowa.
Agbo ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP a Inugu. Ya ce za su shigar da kara kan lamarin a mako mai zuwa.
Idan za a iya tunawa dai, a watan da ya gabata ne ‘yan majalisan LP su shida suka bayyana ficewa daga jam’iyyar zuwa PDP. ‘Yan majalisan sun bayyana sauya shakarsu ne a lokacin zaman majalisa.
‘Yan majalisan da suka sauya shakan sun ce sun dauki wannan matakin ne sakamakon rashin jituwa da rikici da ke cikin jam’iyyar LP a kasa da kuma dukkan jihohin Nijeriya.
“Abun takaici, jam’iyyar ta fada cikin rashin jituwa da rarrabuwar kayuna da suka kai ga kotuna tare da lalacewar ikidan mutane. A baya, jam’iyyar ta kasance tana da akidu masu kyau, amma a halin yanzu rikicin cikin gida ya sa ta samu nakasu tun bayan kammala zabe.”
Sun kara da cewa rikicin Abure da Apapa da na ma’ajin jam’iyyar na kasa sun kara haddasa rarrabuwar kawuna a jam’iyyar. Sun bayyyana fatansu cewa PDP za ta zama musu tsani da za su ci gaba da cika burikan mutane, sannan sun kuma gode wa shugabannin LP bisa goyon bayan da suka samu.
Cikin wadanda suka sauya shekan sun hada da mai tsawatarwa na majalisar jihar mai wakiltar mazabar Igboeze na arewa, Hon Ejike Eze da jagoran majalisar jihar mai wakiltar Inugu ta arewa, Hon Johnson Ugwu da dan majalisa mai wakiltar Inugu ta kudu, Hon Princess Ugwu.
Kazalika, kungiyoyin fararen hula sun shigar da kara a babban kkotun tarayya da ke Fatakwai bisa kalubalantan ‘yan majalisa 27 na PDP da suka sauya sheka zuwa APC.
Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas ta bayyana cewa kwanan nan za ta shiga kotu na neman aiwatar da kundin tsarin mulki kan ‘yan majalisa 27 da suka sauya sheka.
Baban sakataren yada labarai na PDP,Tambari Sydney Gbara, shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP a Fatakwai. Gbara ya ce tuni aka ayyana kujerun ‘yan majalisan 27 a matsayin babu kowa.