Masu shaidar karatun babbar difiloma ta kasa da aka fi sani da (HND)da suka yi makarantun fasaha da wasu makarantu a fadin tarayyar Njeriya suna iya rasa dama ta tafiya yiwa kasa hidima’ (NYSC) saboda sabon tsarin manufar da aka fitar ya nuna cewa dole ne sai an samu satifiket na shaidar yin sanin makamar aiki na shekara daya, kafin wadanda suka halarci irin wadancan makarantu a yarda masu su tafi yiwa kasa hidima.
Hukumar ta NYSC, ta kafar sadarwarta ta Facebook ta bayyana wadanda suka mallaki HND dole su nuna sheda cewa sun yi sanin makamar aiki na shekara daya kafin ayi masu rajista a wuraren da aka tura su yiwa kasa hidima.
- Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Na Duniya Da Rahoto Gaskiya Kan Nijeriya
- Cututtukan Da Suka Fi Addabar Kajin Gidan Gona Lokacin Damina
Sanarwar ta nuna, “Wadanda suke da babbar difiloma ta kasa (HND) ana bukatar da su nuna shedar sun kammala yin shekara daya ta sanin makamar aiki, bugu da kari tare da satifiket da sakamakon jarabawa na ND HND.”
Wannan na nuna kenan wadanda suka kammala makarantun fasaha da makamantansu wadanda za su je aikin yiwa kasa hidima na Batch B stream II,ba tare da shedar da ke nuna sun yi sanin makamar aiki na shekara daya,ba za su tafi aikin yiwa kasa hidima ba.
Wannan sabon tsari na nuna ba tare da satifiket mai nuna an yi aikin sanin makamar aiki na shekara daya, masu shaidar babbar difiloma ta kasa HND,ba za su samu damar yin aikin yiwa kasa hidima ba, da za a fara yin rajista ranar 28 ga Agusta 2024.
Binciken da LEADERSHIP ta yi ya nuna dole ne aikin sanin makamar aiki na shekara daya ne abinda ake bukata kafin amincewa tafiya yiwa kasa hidimam kamar yadda abin yake a dokar hukumar.
Dokar ta nuna wadanda suka kammala makarantun fasaha da makamantansu dole ne sai sun yi aikin sanin makama na shekara daya, wanda satifiket ne zai sheda cewar sun yi kafin a basu damar samun gurbi na karatun babbar difiloma, ana son makarantar ta tabbatar da hakan kafin ta bada damar yin hakan.
Sai dai kuma kash! Ya samu labarin yawancin makarantu amsu bada shaidar babbar difiloma ta HND basu tabbatar da hakan ba kafin su bada gurbin karatun ,yanzu sun yaye dubban dalibai wadanda yanzu suna cikin ni ‘yasu dangane zuwa yi ma kasa hidima NYSC.
Har ila yau binciken ya nuna shekarun baya wasu makarantun fasaha sun yi watsi da dokar,inda suka ba dalibai damar karatu ba tare da sun tabbatar da akwai satifiket na aikin sanin makama na shekara daya ba.
Da take bada dalili shugabar ofishin NYSC ta Jihar Legas,Yetunde Baderinwa, ta ce, “An gano bada dadewa ba wasu makarantun sun bada damar gurbin karatu, ba tare da tabbatar da bin tsarin aikin sanin makama ba na shekara daya.
“Dole ne sai sun yi aikin sanin makama na shekara daya tare da shedar sun yi hakan kafin a bsu damar su samu gurbin yin tsarin karatu na HND, dole ne kuma makarantun su yi hakan kafin su basu damar yin karatun na HND.”
Sai dai kuma wasu daga cikin wadanda suka kammala HND abin ya shafe su, sun yi roko a yi masu ahuwa suna bukatar NYSC ta shiga cikin lamarin tayi wa makarantun su magana a kyalesu , su tafi yi wa kasa hidima, domin an riga an sa su cikin Batch B Stream II.
Sun ce makarantu ne ke da laifi saboda sun basu damar karatu ba tare da sun tantance ko sun yi aikin sanin hidima na shekara daya ba, ko sanar da su akan bukatar da su yi hakan.
Yayin da suka gana da LEADERSHIP wasu daga cikinsu sun nuna rashin jin dadi, na cewar basu da satifiket mai nuna cewar sun yi aikin sanin makama na shekara daya, ballantana ace su je su yi rajistar lokacin da aka bude damar rajista ta yi wa kasa hidima a wannan watan.
Wadda ta kammala makarantar fasaha ta JIhar Kaduna wadda tace sunanta Hauwa, cewa ta yi ta kagara ta tafi aikin yiwa kasa hidima, bayan ita hukumar NYSC ta kira ta, wancan sanarwar ce ta bata lamarin.
Ta ce, “Ina mai matukar farinciki in fara in fara yi wa kasa hidima sai dai kuma damuwata it ace ba za a tantance ni ba (admitted) lokacin da za a fara ranar 28 ga watan Agusta 2024 saboda bukatar satifiket na sanin makamar aiki na shekara daya.Makaranta ta bata yi mana bayani ba mu samar da satifiket din wanda yake dole ne, tsoro na shi ne lamarin na iya sa ace ba zan tafi ba.