- Manyan Abubuwan Da Zaben Ya Bambanta Da Su
- Waiwaye Game Da Siyasar Jamhuriyoyin Baya
- Yadda Muka Shawo Kan Hatsaniyar Orubebe A 2015
- Mukan Ajiye Bambancin Jam’iyya Idan Aka Zo Batun Arewa
A ranar Alhamis 6 ga watan Oktobar 2022, shirinmu na Barka Da Hantsi Nijeriya da muke gabatarwa a Manhajar Podcast ya karbi bakuncin mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, DAKTA HAKEEM BABA-AHMED, inda aka yi tattaunawa ta musamman game da harkokin zaben 2023.
A cikin shirin, ya bayyana wasu abubuwa da dama game da zaben 2023 tun daga kan yakin neman zabe har zuwa zaben kansa. Kana ya yi waiwaye a kan irin siyasar da aka gudanar a jamhuriyoyin baya a Nijeriya har ma da yadda suka shawo kan hatsaniyar da wakilin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a wurin tattara sakamakon zaben 2015, Mista Orubebe ya tayar yayin da ya ga dan takararsu zai sha kasa.
Akwai karin wasu abubuwa da dama, kawai a karanta hirar har zuwa karshe a ji kamar yadda YUSUF SHU’AIBU ya kalla ya rubuta kamar haka:
Ya kake kallon yadda aka fara gudanar da yakin neman zabe a bana?
Wato wannan zaben da za a yi yana da abubuwa guda uku wadanda suka bambanta da sauran hada-hadar zabe. Na daya dai, an canza dokar zabe tare da kara tsawon lokacin yin hada-hadar zabe kamar irin su taron gangami na neman magoya baya da yawace-yawace yakin neman zabe da irin kamfe da ake yi a rediyo da talabijin wanda aka kara shi zuwa kwana 150 fiye da wata uku, wanda ya kasance dogon tsere ne.
An fara shi tun daga yanzu kuma ina tsammanin za a ci gaba har ya rage mako guda ko biyu kafin fara zabe, wanda abubuwa da yawa na iya faruwa kuma zan fada wasu da ke da muhimmanci.
Na biyu, ba mu taba yin zabe wanda manyan jam’iyyu suka shiga cikin irin wannan hada-hadar yakin neman zabe da rikice-rikice a tsakaninsu ba. A baya sukan warware wadannan rikice-rikice lokacin da aka fitar da dan takara, amma har yanzu ana nuna wa juna yatsa.
Na uku kuma, Akwai kuma damuwa na yuwuwar amfani da addini da bangaranci da kabilanci a cikin wannan zabe fiye da kowani lokaci.
Magana na karshe kan wannan zabe da ya bambanta da sauran zabuka shi ne, yadda aka fito da wani salo na gurbata zabe, wanda za a bari a je har inda mutum yake da katin zabe a ba shi kude a ce masa ya dangwala a nan, wato wakilan jam’iyya wadanda aka dora musu amanar su nesanta musu jefa kuri’a da sauran jama’a su suke yin haka.
Ka san yadda ake yi za ka zo a tantance ka a tabbatar cewa ka cancanta ka yi zabe, sannan ka koma gefe, idan aka shirya zabe sai ku yi layi, ga wanda zai ba ku takardun jefa kuri’a, sai ka dauke ka je wurin da za ka dangwala wanda ake so sai ka saka a cikin akwatin zabe.
Yanzu kuma an fito da wani tsari na banza wanda tun ana yi kadan-kadan har ya zama ruwan dare. Inda ake ce wa mutum ga dubu daya ko biyu ko biyar ka dangwala wa wannan.
Takamaimai su waye suke yin wannan abun?
Dukkan jam’iyyu suna yi. Mutane ne wadanda aikinsu kenan.
Suna bangaren hukumar zabe ne ko kuma suna bangaren jami’an tsaro?
Ba sa ko daya, amma da yardarm jami’an hukumar zabe da kuma jami’an tsaro. Domin ba a ma yarda wani ya kusanci wanda yake zabe ba.
Kamar yadda na fada maka, za ka je wurin zabe sannan ka bi layi, idan aka zo kanka, sai ce kawo katinka a duba abubuwan da ake bukata domin a tabbatar ka cancanta katinka ne kuma akwai sunanka a rubuce, sai a ce je ka tsaya can ko je ki tsaya a can a jira.
Idan aka zo yin zabe kuma kai kadai daga kai sai Allah, sai katin jefa kuri’a, sai kuma akwatin zabe. A tsakanin wannan wurin, akwai wadanda za su zo su bayar da kudi domin dangwalawa wani, wasu ma har sai sun dauki hoton wand aka dangwalawa.
Wanda shi ake kira sayan kuri’u kuma ana amfani da shi a jihohi da yawa, da alama wannan zabe za a yi irin wannan abu.
Misali, wani zai iya cewa da wace jiha da wace jiha wannan abu ya faru?
Ya faru a zabukan da aka yi kamar na jihohin Osun da Ekiti da kuma Anambra, kuma dukka abin da jam’iyyu ke shiryawa har da wannan abu a ciki, sannan akwai kudaden da aka killace domin shi.
Magana na karshe shi ne, za a yi zabe wanda yake da mummunan matsala wata kila ma a hana wasu wurare yin zaben, saboda rashin kwanciyar hankali na rashin tsaro.
A nan arewa akwai jihohi kamar irin Kaduna, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Neja, wurare da yawa saboda barazanar ‘yan ta’adda wadanda suke rike da kauyuka suna iya hana zaben gaba daya.
Ita wannan gwamnatin ta yi alkawarin cewa kafin zaben za ta magance wannan matsalar tsaron?
Ita wannan gwamnatin ta yi alkawarin za ta yi abubuwa da yawa amma ba mu ga ta yi ba, muna jira Allah ya sa. Amma dai a yanzu halin da muke ciki a jihohin kudu maso gabas akwai jihohi biyar da kungiyar IPOB suke rike da su, wanda ko nunfashi a wasu wuraren ba a yi sai sun ce a yi.
Su ne masu cewa a zauna a gida a duk ranar Litinin kuma ba za a fito ba, wanda sai an yi yaki da su kafin ma su bari wasu bangarorin mutane su yi zabe, a yanzu suna cewa ba za su bari a yi zabe ba.
Kuma babu wani jami’in tsaron da zai iya cewa daga Sakkwato zuwa Abiya, sanna daga Leagas zuwa Borno za a iya tabbatar wa duk dan Nijeriyan da yake da katin zabe zai je ya yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kuma cikin wata hudu zuwa biyar yayda wannan rashin tsaron ya yi zurfi, dole mu sa barazanar rashin tsaro a cikin lissafin abubuwan da za su addabi zaben da za a yi.
Amma Dakta akwai wadanda suke ganin gwamnati ta saba idan za a yi zabe za ta cika jami’an tsaro, misali za ka ga an kai jami’an tsaro dubu talatin ko dubu kaza.?
Sai zaben jiha ba. Ai kwasowa ake a jihohi a tara a wuri daya saboda zaben jiha daya ce. Shi ya sa ake yin sa asalun-alun yankan jaki. To kuma wannan ‘yansandar gaba daya raba su za a yi kasan.
Kuma akwai wani abu idan ka sani game da zabe domin ni na yi sakataren INEC, kashi kusan 70 cikin 100 na mazaba, ballantana a halin yanzu an kara mazabu kusan dubu hamsin, inda wani wurin mutane ne ke tsare mazabun ba ‘yansanda ba ko kuma ka ga dan sanda guda daya ko dan kato da gura, to wani aiki mutum zai yi. Idan mutum biyar suka zo ba su san a yi zabe suna iya tayar da wurin.
Tun da ka kawo wannan magana ta matsalar tsaro kuma abu ne wadda yake ciwa mutane da yawa tuwo a kwarya, mene ne ‘yan Nijeriya ya kamata su yi a kan wannan sha’anin tsaro lokacin zabe?
‘Yan Nijeriya babu wani abin da za su iya yi sai dai mu yi addu’a, abin da ya rage a hannun gwamnati. Ita hukumar zabe tana iya bakin kokarinta kuma muna yaba mata. Domin akwai abubuwa da yawa da ta yi na gyara ta yadda muke yin zabe da bayyana sakamakon zabe muna yaba mata. Amma komi ya rage a hannun gwamnati.
Idan ana so a yi zaben nan jama’a su fito hankali a kwance, kuma a fito da sakamako wanda zai gamsar da jama’a, to damarar da za a yi domin a tabbatar cewa inda duk rashin tsaro ke barazana kamar wuraren da ‘yan ta’adda suke da ikon hana zabe a yi maganinsu.
Kamar a je yankin kudu maso gabas a yi maganin ‘yan kungiyar IPOB, sannan a je wasu wurare inda ba a tsoron dan sanda ba a tsoron gwamna ba a tsoron sarki wanda mutane ka iya cewa ba za a yi zaben ba, musamman idan aka samu rashin jituwa ko aka samu hatsaniya wurin hada-hadar zabe, wanda zai kai akwai inda wasu mutane za su ce tun da ba ku bari namu ya zo ya samu goyon ba yaba ba, mu kuma naku ba zai zo ba sai a samu tashin hankali. Idan haka yi wannan, to zai shafi zaben domin akwai inda za a iya hana zaben gaba daya, saboda wannan tashin hankalin yakin neman zabe a yanzu haka an ma fara kadan, amma zai kara muni.
Wane ga kabilarshi ya je wurinku yakin neman zabe kun ce ba zai yi ba, to muma naku ba zai zo ya yi yakin neman zabe a wurinmu ba.
Akwai wuraren da za a yi mummunan tashin hankali, idan na wane ya zo zai yi kamfen a nan mu kuma ba za mu barshi ba, kuma idan har ya zo za a yi fada.
To ana gani kamar yanzu kamfen bai riga ya kankanma sosai ba, misali shi Peter Obi ya tafi Jihar Filato kuma ga shi jiha ce ta arewa wanda ya kaddamar da kamfen, tun da abun bai yi nisa ba kuma ka ce an fara, to ta ina ne aka fara, misali a ce ya tafi wani yanki kuma aka ce ba zai yi kamfen ba?
Ai hange nake yi ga alamomin da ke kasa. Kayar yadda na fara gaya maka muna da kana 150 ana gudanar da kamfen, ba mu ga komi ba tukunna ka bari a fara manya-manyan hada-hadar zabe.
Amma abubuwan da muke gani a kasa yanzu akwai inda ake cewa kar ma ku zo gaba daya. Akwai inda ko an ce maka ka ce ba za ka fara zuwa ba. Yanzu mutanen Zamfara da na Kaduna da ke Birnin Gwari da Giwa da dai sauransu da ke cikin tashin hankali wani dan siyasa ne zai je musu kamfen ko mai neman gwamna ne, kai ma wakilinsu ne.
Ka tambaye ne wani abubuwa ne na hango a cikin wannan zabe ko zai bambanta da sauran zabukan baya, shi ne nake fada maka abubuwan da suka fito na wannan zabe wanda ya kamata mu jama’a mu yi la’akari da su, sannan gwamnati ta yi la’akari da su wanda za su yi barazana kuma suna iya kawo cikas a kan kyautatuwar zabe da ingancin zabe da kabuwarsa da tashin hankali wanda muke addu’a Allah ya kiye a lokacin zabe da bayan zabe.
Tun da su wadannan masu dauke da makamai za su yi barazana da wannan zabe, akwai yuwuwar wasu ‘yan siyasa za su yi amfani da su domin su ci zabe a wani wurin?
Eh mana, akwai mana. In yanzu ni ina da hanyar da zan yi in zo wuri in ce kar ku bar wani ya zo ya yi hada-hadar kamfen ko kuma ana wa mutanensa su fito ko ba ma so a zabe shi kuma ina da bindiga babu wani wanda ya fi ni karfi wanda zai iya cewa mutane ku fito, zan yi. Matsalar a nan ita ce, tsaro yana da matukar muhimmanci kan tabbatar da cewa jama’a sun sauke nauyin da ke kansu kuma gwamnati ta ba su dama su yi zabe.
Idan yanzu daga nan zuwa wata biyar zuwa shida gwamnati ta share wadannan abubuwan daga Borno zuwa Yobe na matsalar Boko Haram da arewa maso yamma na sace mutane da ‘yan ta’adda da dai sauransu tare da gyara hanyoyi wanda za ka iya tafiya a ko’ina babu tsoro, sannan mutanen da ke karkara za su iya jefa kuri’arsu kuma jami’an zabe za su gudanar da aikisu ba da tsoro ba, shi ne abun dubawa.
Yanzu jami’an tsaro nawa ne za su iya zuwa wasu wurare a Zamfara domin gudanar da zabe. Sanna mutane nawa ne za su iya zuwa Birnin Gwari su yi zabe.
Akwai alamar da ake gani na cewa wannan gwamnati ta yi hobbasa na ganin yadda su ‘yan Boko Haram suna ta mika wuya, idan ba a manta ba a ‘yan makanni da suka gabata shi babban mai kisa na kungiyar gaba daya ya mika wuya shi da iyalinsa.
Sannan a shiyyar arewa maso yamma a kwanakin baya mun ji cewa shi babban dan bindigan da ake fargaba, Bello Turji an kai masa farmaki wanda aka warwatsa mabuyarsa. Ba ka ganin wadannan alamomi ne na samun nasarar zaben?
Alomomi ne kuma Allah ya sa su ci gaba. Ai mu abin da muke so kenan kuma muna wa gwamnati addu’a Allah ya ba ta nasara ta ci gaba da samun nasarori daga nan zuwa lokacin zabe.
Kungiyarku ta dattawan arewa ta kafa sharudda da dan takarar da ‘yan arewa ya kamata su zaba, wadanne sharudda ne wannan?
Sharudda ne wadanda suka shafi mu al’ummar arewa kan abubuwan da muka ganin muna bukata ga kowani mutum wanda zai zama shugaban kasa. Kuma ba sharudda ba ne kawai wadanda za mu buga a jarida ko mu fada a gidan rediyo, zuwa za ka yi ka zauna tare da mu domin mu yi maka tambayoyi ka amsa mana kai ma idan kana da tambayoyi sai ka yi mana mu amsa maka. Idan Allah ya yarda saura kwaniki goma mu fara ga ‘yan takara shida cikin goma sha takwas, sannan duk wani wanda yake so ya zo sai ya zo.
Za mu tambayeka me za ka yi domin maganin tsaro wanda ya addabi mu takai ya lalata mana tattalin arzikinmu kuma ya lalata mana zamantakewa tare da watsa mana mutanenmu.
Me za ka yi mana kan tattalin arzikin arewa da ya dagargaje, sannan me za ka yi mana a kan ‘ya’yanmu wadanda ba sa zuwa makaranta, domin a yanzu idan aka tara yara wadanda ba sa zuwa makaranta gaba daya a arewa Boko da Islamiyya kusan sun kai miliyan 33 kuma wannan ba karamin abun tsoro ba ne.
Idan aka kalli yawan yaran da ba sa zuwa makaranta kuma ba sa wani sana’a da zai taimaka musu diniya da lahira, nan da shekara 20 yaya arewan nan za ta zama, ka ga abun damuwa ne. Za mu tambayeka ya za ka yi mulki kuma da wa za ka yi, sannan kana da wani tsari da zai farfado mana da hanyoyin magance matsalolinmu, duk irin wadannan tambayoyi za mu yi masa daga mu sai shi kuma ya kawo mana gaskiyar lamari.
Shi ya sa ka ga kungiyar dattawan arewa tana daya daga cikin wadanda ba su fito sun ce ga nata dan takara ba.
Ku a cikin kungiyar dattawan arewa akwai wadanda suke mara wa wasu jam’iyyu baya, misali yanzu kai dan jam’iyyar PRP ne, to kuma ana iya samun wasu a ciki ‘yan PDP wasu kuma ‘yan APC ne, to ta yaya za a yi ba za ku nuna muradin dan takararku ba?
Idan aka zo maganan arewa ba mu tuna jam’iyya.
Babu ruwanmu da bambancin jam’iyyunmu muna duba wanda zai iya magance tattalin arzikin arewa da matsalar tsaro da ta ilimi da dai sauransu. Muna duba wanda zai iya farfado da arewa da kuma muatanen arewa a kowani jam’iyya yake.
Lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki ana cewa Nijeriya ta samu shugabanci, amma ashe shi mulkin kawai yake so ba ya yi jagagorancin kasa domin ya gyara ba.
Duk abubuwan da yake yi na kokarin farfado da tattalin arziki kamar shirye-shirye da yake kawowa na tsarin kasafin kudi mai dogon zango da yake hada shekaru da yawa da kuma shirinsa na farfado da tattalin arziki har ya kai wa majalisa?
Yanzu ina ka taba jin an ce gwamnatin dakyar take iya biyan albashi saboda bashi yana kokarin ya durkusar da ita, wai za a je a kai kasafin kudi na tiriliyan 19 amma cikinsa akwai bashi ko gibi na tiriliyan 13, ai abun ya zama tatsuniyar yara domin yaudara ne kawai ake yi wa mutane, wanda duk ya san yadda ake yin kasafin kudi aka ce maka ba ni da kudi amma ga abin da zan kashe.
Kai ka san cewa sauran ko ba za a yi ba ko kuma bashi za a nemo. Bashi ya riga ya yi mana kanta a Nijeriya kowa ya sani, jikokinmu ma sai sun biya wannan bashi.
Bashi ba illa ba ne domin Hausawa na cewa. ‘Bashi hanji ne kowa yana da shi a jikinsa’, amma akwai bashin da jiki bai zama sai an ci. Wannan gwamnatin sai dai Allah ya raba mu da ita lafiya.
Kana daya daga cikin wakilan jam’iyyar APC a wurin tattara sakamakon zaben 2015, lokacin da shi dan bangaren PDP, Mista Orubebe ya so ya tayar da wannan hatsaniyar ya hargitsa tattara sakamakon zaben, ta yaya kuka iya tafiyar da kanku ba ku mayar da martani wanda zai hargitsa wurin ba? muna so mu ji hikimar da kuka saka a wannan lokacin.?
Gaskiya akwai abubuwan da ba zan iya gana maka ba a nan, amma zan iya gaya maka wasu. Ni na samu labarin za a yi wani abu kamar haka, an fara wannan tantance zaben ne lokacin da ake kawo sakamako a dakin taro na kasa da kasa, inda aka shafe kanaki uku zuwa huku kuma a nan muke kwana na tsawon wannan lokaci babu mai zuwa ko’ina tun da a kan dauki lokaci idan an kawo jiha guda daya ko biyu, sai an dauki wasu awoyi.
Daf da ranar Litinin da yamma mun riga mun san waye ya ci zabe, tun da idan an kawo sakamakon aka fada za a manna ne kuma duk duniya na gani, mun sani a cikin daren na ji kishin-kishin cewa gobe wasu na cewa ba za a bayar da sakamakon zabe ba.
Shi kuma doka ta ce idan ba shugaban hukumar zabe da kansa ya tashi ya ce a kan lissafin da aka yi a gaban kowa wanda aka tara na wane da na wane, abin da muka gani a yayda doka ta ce, ni a matsayina na babban mai fadan sakamakon zabe wana ne ya ci. Idan ba a yi wannan ba, to zabe bai yuwu ba.
Abin da aka yi wa Abiola kenan. A rubace kam Abiola ne ya lashe zabe, amma shi shugaban zabe bai zo ya fada ba, kuma doka ta ce sai an fada.
Akwai tsarin da ake yi na hana wannan, amma ba mu san komi ba. Mun ta gudanar da bincike-bincikenmu har muka cewa ko kila irin na Abiola suke kokarin shiryawa.
Akwai ‘yansanda a wurin da ‘yan jarida da wakilan duk wani dan takara, lokacin mu 26 ne wadanda suke je su wakilci ‘yan taka. Mu biyu da ni da Sanata Mamora wanda a yanzu minista ne yanzu, muka wakilci shugaban kasa Buhari.
Mun ta kokarin mu ji me ake shiryawa, a ce mana idan kuna so ku kawo kudi da kaza da kaza domin abubuwan da suke cewa a kawo suna da yawa kuma ba mu da shi, kuma ba za mu yi alkawarin da ba za mu cika ba.
Sai muka yi kokarin rada wa su manya-manyan hukumomin zabe da kuma ‘yan jarida cewa akwai wani abu da ake shiryawa ba mu san ko mene ne ba amma mu yi hattara. Kila kokari za a yi a tayar da hayaniya ko a tunzura jami’an tsaro a dan yi wani abu idan ya so a fasa fadan sakamakon zaben.
Wannan abun shi ya taimakemu. Da muka ga sun fara wannan ba su yarda ba a tashi da a koma ofis domin su ba su yarda ba, sai muka ce abun ya bayyana, wasu na cewa a je a nuna musa iyakarsu, sai muka ce a kyalle su abin da suke so mu yi kenan a yi fada a wurin tare da fashe-fashe shi kenan bukatarsu ta biya. Kuma shi dokar zabe lokacin da aka kayyade dole a fada wanda ya ci zabe, idan ya wuce wannan lokacin, to babu zabe kuma babu shugaban kasa.
Za mu so yin waiwaye kamar abubuwan da suka gudana lokacin zabe a jamhuriyoyin baya, misali lokacin Shagari, idan kuma za a yi mana waiwaye kan jamhuriya ta farko ma, saboda wasu da yawa ba su san tarihi ba, misali kamar ire-irenmu da muka taso yanzu, ko za a dan yi bitar wadannan?
To ka ga shi zabe a da lokacin su Sardauna da sauransu, sarakuna suna da bakin fadi a ji da yawa.
Jam’iyyar NPC tana da karfi ta karbu wurin wadanda suke da sarauta da ma su mulki a hannunsu sai ta yi amfani da su. A arewa jam’iyyar da ta fi hamayya da ita ce NEPU ta talaka, ita kuma tana amfani da karbuwarta wurin talaka, domin talaka na shan wahala a hannun ‘yan NPC.
Ana matukar wahalar da dan NEPU, idan ka fito a ce kai dan NEPU ne, to zak a ji jiki saboda kana ja da masu iko.
Kudu na jin zafin arewa saboda yawanta da hadewarta, domin kullum aka tashi neman zabe, sai a ce ku je arewa ku yago wadanda ba Hausawa ba musulmai ba.
duk zaben da ake yi Awolowo kokarinsu kenan kuma har yanzu wannan shirin yana nan, sai a ce ai ga inda mutane suke ku je ku rage karfin arewa ku dibo wadanda suka bambanta.
Kabilanci da addinanci tun da aka kafa Nijeriya yana cikin irin siyasarmu bai taba fita ba. Lokacin Shagari, wanda sojoji sun dade suna kan mulki har aka fara sabawa da siyasa ta yi sanyi ta koma kusan sai yadda sojoji suka ce, sai aka sake taso da ita har Shagari ya lashe zabe ya dauko mataimakinsa dan kabilar Ibo, kuma a lokacin an gama yakin basasa kusan shekara tara, domin an yakin basasa a shekarar 1970, inda suka yi aiki tare lami lafiya.
Sojoji da yake sun ji dadin mulki abun ya shiga musu rai, shekara hudu zuwa biyar suka bari ana mulkin farin huda, inda suka sake dawowa kan karagar mulki mai tsawo, kuma ba wani hujja suke da shi ba, kawai dai sun dandana abun suka ji yana da dadi.
Kuma wanda ya yi wannan juyin mulki shi ne Buhari na yanzu, wanda ya dawo yana neman a sake ba shi mulkin dimokuradiyya, inda shi ma ‘yan’uwansa sojoji suka ture shi wasu kuma suka karba har ya kai dai lokacin zabe na 1999, wanda sojoji da kansu suka san cewa ba zai yuwu su ci gaba da mulkin Nijeriya ba, domin ruwa ya kare wa dan kada. Suka ce ina ‘yan siyasa, inda manyan-manya daga arewa suka fito suka ce ga ‘yan siyasa idan har su kuke nema.
Suka ce maganin wannan abu shi ne, tun da Yarbawa na bore a kan cewa daya daga cikinsu wato Abiola ya ci zabe an hana shi, a ba su Nijeriya domin su cece ta, inda suka ce mu arewa taimaki Bayerabe ya zama shugaban kasa kuma mu nemi irin namu wanda za mu yarda da shi. Inda suka dauko Obasanjo, wanda Obasanjo ya taba karbar mulki lokacin da aka kashe Murtala, inda ya yi shekara uku kuma ya nuna alaman kamar zai yi adalci a Nijeriya, domin arewa ta san shi.
Manyan ‘yan siyasan arewa su suka yi wa Obasanjo kamfe su suka kakkabe shi tare da saka masa riga da turare daga gidan yari wanda aka yi masa daurin rai da rai, amma aka sako shi tare da gyara shi har aka yi masa jam’iyya ta PDP, aka ce arewa ga naku, Yarbawa suka ce tir ba su yard aba. Sai arewa suka ce idan mun yarda shi zai yi, kuma haka aka yi.
Tun farko shi ‘yan’uwansa Yarbawa ba su ba shi gayon baya ba?
Ko daya. Zuwansa na fari cikin shekara hudu kafin ya kammala mulki, ya juya abin yadda su suke kwalayinsa.
Da aka yi zabe a 2003 zuwa 2007, jiha daya ce kawai bai kama ba, domin a lokacin da ya zama shugaban kasa gaba daya jihohin Yarbawa babu wacce ta zabe shi, amma da yake mulki na da dadi kuma idan kana mulki kana iya gyara wa mutanenka abubuwa ba irin yanzu ba.
Da ya gane cewa idan na yi musu kaza da kaza a kadan-kadan cikin shekara biyu zuwa uku ya juye musu da kwakwalwa, inda suka koma cewa nasu ne. Da aka sake zabe jiha daya ce PDP ba ta kwace ba ita ce Jihar Legas, inda Tinubu yake.