Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki mai zaman kanta (SERAP) ta yi barazanar gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu idan har ta gaza gudanar da bincike kan zargin bacewar sama da ganga miliyan 149 na danyen man fetur.
Kungiyar SERAP ta fito karara ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari barazana a wata wasika mai dauke da kwanan watan Afrilu 22, 2023, inda ta bayyana cewa tana bukatar gwamnati ta kafa kwamitin bincike na shugaban kasa da zai gaggauta gudanar da bincike kan wannan zargi.
Kungiyar ta kuma bukaci shugaba Buhari da ya tabbatar da hukunta duk wanda ake zargi da hannu wajen wawure dukiyar man kasar nan tare da kwato duk dukiyoyin da suka wawure.