Shahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi wanda ke cikin kusoshin kungiyar Muslim Brotherhood ya rasu.
BBC ta rawaito cewa, tsohon shugaban kungiyar kuma Limaman Musulunci na duniya ya rasu ne yana da shekaru 96.
- Saudiyya Ta Ja Kunnen Netflix Kan Yada Fina-Finan Da Suka Keta Dokokin Musulunci
- An Kama Sojoji 2 Kan Zargin Suna Da Hannu A Kisan Wani Malamin Addinin Musulunci A Yobe
An haife shi a Masar kafin ya koma Qatar da zama.
Talla
Youssef al- Qaradawi ya wallafa litattafan musulunci da dama.
Yana gabatar da shirin talabijin a tasha al-Jazeera kuma miliyoyin mutane ne ke bin wa’azinsa a fadin duniya.
Talla