Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal.
Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa.
- Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola
- Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya
Shakirat, wadda ke taka leda a Bayelsa Queens, ta kuma haskaka a gasar Premier ta mata ta Nijeriya (NWFL), inda ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar wa ƙungiyar nasarar lashe kofin a watan Mayu. Haka kuma ta kasance cikin manyan ƴan wasan da suka zura ƙwallo a wasan neman shiga gasar zakarun mata ta WAFU B a ƙasar Cote d’Ivoire.
Zaɓenta cikin jerin ƴan wasa uku na ƙarshe ya ƙara tabbatar da tasirinta a ƙwallon ƙafa, tare da mayar da ita daya daga cikin fitattun matasan ƴan wasa da ke tasowa a nahiyar Afrika.














