Kasashe masu tasowa na fama da yawan mace-macen mata masu juna biyu da jariran da ake haifa saboda yawan matsaloli da ake samu tun daga rainon ciki har zuwa haihuwa.
Wasu na rasa rayukansu saboda sakaci na iyalansu, wasu kuma na rasa rayukansu ne saboda sakaci irin na likitoci da ungozoma a asibitoci.
- NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba
- Yadda Barakar PSG Ta Sake Fitowa Fili
Dokta Abdulsalam Muhammad, kwararren likita ne da ke kula da mata masu juna biyu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), ya bayyana wasu abubuwa da ke haddasa yawan mace-macen da kuma wasu wahalhalu da sauran hanyoyi da masu juna biyu ke jikkata.
Likitan ya fara bayani ne kan yadda ciki yake da kuma lokacin da yake kai wa har zuwa lokacin haihuwa ko kuma nakuda.
Daga ciki akwai batun karbo rubutu da ya yi, wanda ya bayyana cewa sun yi bincike kan lamarin kuma sun samo sakamako.
“Mun lura yanzu ana samun matsala idan aka kawo mace haihuwa, ko da kuwa tana zuwa asibiti kuma tana bin duk dokokin da aka gindaya mata, amma kuma daga baya za a samu matasala lokacin da nakudar tai nisa ko kuma bayan ta haihu.
“Daga cikin abin da muka lura shi ne duk wata mata da aka kawota asibiti kuma tai amfani da wani ruwa, wanda suka bayyana da cewa rubutu ne, to sai ta samu wannan matsala.
“Ko dai matsalar yawan zubar jini, ko kuma rubewar mahaifa ko kuma ma rasa rai a tsakanin mai juna biyu da kuma jaririn da aka haifa.”
Wadannan matsaloli da ya ambata dai su ne kanwa uwar gamin da ake ganin su ne suka fi bayar da matsala ga mata a kasashen da suke tasowa, saboda karancin wayewar harkar kiwon lafiya ko kuma sakaci dangane da yadda asibitin yake.
“Daga karshe bincikenmu ya gano cewa wannan rubutun da mata suke amfani da shi lokacin da suka fara nakuda ko kuma dab da haihuwa ba rubutu ba ne! Wata kwayar magani ce da ake kira da ‘Misoprostol’ wadda ake amfani da ita a asibiti yayin da mace ta kasa haihuwa da kanta, kuma ana sa rai za ta iya haihuwar ba tare da an mata aiki ba”, in ji Dokta Labaran.
Har wa yau, ya yi tsokaci kan wannan magani da ake cewa rubutu ne a cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan rediyon Freedom da ke Kano.
“Maganin yana da nauyi Miligiram 200, kuma idan za mu yi amfani da wannan maganin muna raba shi hudu ne, sai mu saka wa mace maganin a kasanta, ba ta baki ake ba da shi ba, sai bayan awa shida idan an duba yanayin ta dana jaririn sai a sake saka mata shi.
“To amma mu mun gano cewa masu ba da wannan maganin da sunan rubutu, suna hada kamar kwaya guda 50 ne sai su jika a botiki, sannan sai su zuba a kananan robobi su ringa siyarwa da sunan rubutu.”
Duba mara lafiya da bayar da magani a Nijeriya ba tare da zuwa wajen kwararru ba ya zama ruwan dare, wanda kuma masana lafiya ke alakanta hakan da barkewar cuttutuka a tsakanin al’umma ba tare da sun farga ba.