A ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar 1972, babban taron MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2758, kudurin da ya amince da “Gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin ita ce take da wakilcin kasar Sin a MDD”.
A sa’i daya kuma, ofishin kula da harkokin dokoki na sakatariyar MDD ma ya bayyana a zahiri cewa, “MDD na ganin cewa, kasancewarsa wani lardi na kasar Sin, Taiwan ba shi da ‘yancin kansa.”
A shekarar 1978 kuma, Sin da Amurka sun cimma yarjejeniyar kulla huldar diplomasiyya, inda Amurkar ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati daya kacal a kasar ta Sin, kuma jama’ar Amurka za ta kiyaye hulda da jama’ar yankin Taiwan ta fannonin al’adu, da ta kasuwanci da sauransu, amma ban da ta sassan gwamnati. Baya ga haka, kasashen biyu sun kuma daddale wasu sanarwoyi biyu a shekarar 1972 da ta 1982, inda Amurka ma ta amince da kiyaye manufar kasar Sin daya tak a duniya. Wadannan sanarwoyi guda uku dai sun zama tushen huldar siyasa a tsakanin kasashen biyu.
Sai dai duk da hakan a cikin ‘yan shekarun nan da suka wuce, Amurkar ta rika cewa tana martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, a yayin da kuma ta yi ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, tare da kawar da bayanai na “Taiwan wani bangare ne na kasar Sin” daga shafin majalisar harkokin wajen kasar, baya ga kuma fitar da “dokar hulda da Taiwan” da makamantansu, ga shi kuma a kwanan baya, kakakin majalisar wakilan kasar ta Amurka Nancy Pelosi, ta kare aniyarta ta ziyartar Taiwan, duk da rashin amincewar da kasar Sin ta nuna da babbar murya.
Lallai, hakan ya shaida yadda babbar kasar ta yi amai ta lashe, haka kuma matakin ya zubar da kimar ta a idon duniya. (Mai zane:Mustapha Bulama)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp