Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja fadar gwamnatin Nijeriya, ta sanar da ranar Litinin 18/12/2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ƙulubalantar nasarar lashe zaɓen kujerar gwamna da Gwamna Ahmadu Umaru Fintir ya yi.
Da ma Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ‘yar takarar kujerar gwamna ƙarƙashin Jam’iyyar APC ta daukaka karar, ta na mai kalubalantar hukumar zabe INEC da jam’iyyar PDP da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
- Kotun Daukaka Kara Ta Dage Sauraren Shari’ar Fintiri Da Binani
- Binani Ta Maka INEC A Kotu Kan Soke Ayyana Ta A Matsayin Wadda Ta Lashe Zaben Gwamnan Adamawa
Biyo bayan sauraren daukaka karar da Aishatu Binani da jam’iyyar APC su ka yi, Kotun daukaka karar ta sanar da gobe Litinin 18, ga disambar 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar.