Jam’iyyar APC ta gindaya wasu sharuda kafin dan takararta na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da wata muhawara da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour LP, Peter Obi.
Da yake lissafa sharuddan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, Keyamo ya ce ya kamata Obi ya fara fitar da takardar kudiransa kafin duk wata muhawara da yake bukata yayi da APC.
Ya kuma kalubalanci Obi da ya lissafo nasarorin da ya samu a wa’adi biyu da yayi a matsayin gwamnan jihar Anambra domin kwatanta nasarorin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya samu a lokacin yana Gwamnan jihar Legas.
Keyamo ya kuma bukaci Obi da ya bayar da jerin sunayen mutanen da suke mara masa baya a siyasance tun lokacin da yake gwamna da kuma wadanda suke tare da shi yanzun.
Babban Lauyan na Nijeriya SAN ya kara da cewa, ya kamata Obi ya bayyana sunan wata jam’iyyar siyasar da ya kafa ko kuma ya hada kai da wasu jam’iyyun don kafa wacce yake cikinta yanzun.
Ya kuma kara kalubalantar Obi da ya bayyana gudunmawar da ya bayar wajen dawo da mulkin dimokuradiyya daga mulkin Soja da dorewar dimokuradiyya fiye da Tinubu.
Kakakin jam’iyyar APCn ya bayyana cewa idan aka cika wadannan sharudda, jam’iyyar APC za ta turo wakilanta domin su yi muhawara da Obi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp