“Kasa da kasa su kasance suna zaman daidaito da juna wajen sa hannun gudanar da harkokin duniya da ma yanke shawara da cin moriya” “Kada a tilasta kakaba dokokin cikin gida na wasu kasashe a kan sauran kasashe” “Nuna rashin amincewa da daukar matakai na kashin kai” “A yi kokarin daidaita gibin da ke tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba” “A dauki hakikanan matakai na hadin gwiwa”. A ranar 1 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) Plus a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, inda ya gabatar da Tsarin Shugabanci na Duniya wato “GGI” a takaice, shawarar da ta samar da mafita ga duniyar da ke fama da tashe-tashen hankula a halin yanzu.
A duniyar yau, aukuwar rikicin shiyya shiyya da matsalolin ci gaban tattalin arziki da rashin bin ka’idoji da dokoki da daukar matakai na kashin kai da kariyar ciniki da rashin tsarin shugabanci nagari a duniya, duk suna addabar kasashen duniya. Ta yaya za a inganta tsarin shugabanci na duniya, ya zama abin da ke bukatar a gano bakin zaren warware shi ga gamayyar kasa da kasa. To, faduwa ta zo daidai da zama bisa yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar GGI.
“Ya kamata mu bi tsarin daidaito a kan ‘yancin yankunan kasa sau da kafa, ya kamata mu kiyaye bin dokokin kasa da kasa, ya kamata mu aiwatar da tsarin mu’amala da bangarori daban daban, ya kamata mu yi yekuwar amfani da tsarin da zai fi mayar da hankali a kan al’umma, kana ya kamata mu mai da hankali kan daukar matakai na hakika.” Ka’idoji biyar ke nan da ke cikin shawarar GGI, wadanda suka mai da hankali a kan ainihin matsalolin da ake fuskanta a tsarin shugabanci na duniya, tare da bayyana matsayi da dabarun da suka kamata a dauka domin gyara tsarin. Daga cikinsu “tsarin daidaito a kan ‘yancin yankunan kasa” ya zama tushen tsarin shugabanci na duniya. Kasa da kasa, manya da kanana, masu karfi ko marasa karfi, ya kamata su kasance daidai-wa-daida wajen sa hannu ga harkokin duniya. Ya zama dole a kawo karshen yadda wasu ‘yan tsirarrun kasashe kawai ke fada a ji a harkokin duniya, kuma ya kamata “a kara wakilcin kasashe masu tasowa da fito da muryoyinsu a duniya”, don kara inganta adalcin tsarin duniya. Sa’an nan, dokokin kasa da kasa su kasance masu tabbaci ga tsarin shugabanci na duniya, wadanda ya kamata kasa da kasa su rubuta su, da kiyaye su, da ma aiwatar da su. Har wa yau, yin mu’amala da bangarori daban daban ya zama hanyar da za a bi wajen gudanar da tsarin shugabancin duniya, kasancewar tsarin shugabancin duniya na shafar kowa da kowa, ya kamata a daidaita hadin gwiwa da juna a maimakon nuna fin karfi. Kazalika, ya kamata a mai da hankali a kan al’umma, a sabili da yadda kyautata rayuwar al’umma shi ne jigon ainihin burin da ake neman cimmawa wajen inganta tsarin shugabanci na duniya. Daga karshe, daukar hakikanan matakai ya kasance ginshiki na tsarin shugabancin duniya, don daidaita matsalolin da ke addabar kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa.
Bana ake cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da mulkin danniya a duniya da ma kafa majalisar dinkin duniya(MDD). A shekaru 80 da suka wuce, al’ummun duniya sun hada karfi da karfe wajen samun nasarar yaki da mulkin danniya, kuma kasancewar kasar Sin daga cikin muhimman kasashen da suka cimma nasarar yakin, ta hada kai da kasa da kasa wajen kafa MDD. A yau kuma, lokacin da tsarin shugabanci na duniya ke fuskantar sabbin matsaloli, kasar Sin a matsayinta na babbar kasa da ke kokarin sauke nauyin da ke bisa wuyanta, za ta tsaya tsayin daka wajen kiyaye tsarin duniya da ke karkashin ginshikin MDD, ta hada kai da kasashe masu neman ci gaba, don dada yin kokarin gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da ma tabbatar da zaman lafiya da ci gaba ga dukkanin bil Adama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp