• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarwari 4 Na Kasar Sin Za su Taimaka Wajen Samar Da Sabon Abun Al’ajabi A Asiya Da Yankin Tekun Pasifik

by CMG Hausa
3 years ago
Pasifik

Ranar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cikin jawabinsa a yayin kwarya-kwaryar taron shugabanni mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasifik APEC karo na 29 cewa, yanzu duniya ta sake shiga muhimmin lokaci a tarihi.

Asiya da yankin tekun Pasifik suna kara taka muhimmiyar rawa, yayin da matsayinsu ya samu ingantuwa sosai.

  • Kasashen Tsibiran Tekun Pasifik Sun Fi Bukatar Sahihiyar Gudummawa Daga Kasar Amurka

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda 4 kan yadda za a hada hannu wajen raya makomar bai daya a Asiya da yankin tekun Pasifik a sabon halin da ake ciki, wato kiyaye adalci a duniya, a kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Asiya da yankin tekun Pasifik, da tsayawa kan bude kofa ga ketare da dunkule dukkan bangarori, a kokarin raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai wadata, da nacewa kan raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai tsabta da kyan gani ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tsayawa kan taimakawa juna a Asiya da yankin tekun Pasifik, wadanda ke da makoma iri daya.

Ruhin wadannan shawarwari 4 sun yi daidai da shawarwari guda 6 da Xi Jinping ya ambato cikin rubutaccen jawabinsa a yayin taron shugabannin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC a ranar 17 ga wata.

Dukkansu sun takaita fasahohin da aka samu wajen samar da abun al’ajabi na Asiya da yankin tekun Pasifik, sun kuma tsara manyan tsare-tsare kan halin da ake ciki yanzu. Shawarwarin na da ma’ana mai zurfi kan hakikanin halin da ake ciki.

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Ba za a samu ci gaba ba, sai an samu zaman lafiya tukuna. Kana kuma, ci gaba ya na ba da tabbaci wajen samun zaman lafiya.

A matsayinta na muhimmiyar mambar kungiyar APEC, kasar Sin ta samu ci gaba sakamakon kasancewa a Asiya da yankin tekun Pasifik, yayin da ta ba da nata gudummowa wajen raya Asiya da yankin tekun Pasifik.

Ya zuwa shekarar 2020, jimillar yawan cinikin da ke tsakanin Sin da mambobin kungiyar APEC ta kai dalar Amurka triliyan 2.87. Kwanan baya, an samu nasarar gwajin layin dogon Jakarta-Bandung mai saurin tafiya. An fara aiki da tasoshin dakon kaya a layin dogo tsakanin kasar Sin da kasar Laos.

Kana an fara amfani da babban titin dake tsakanin Phnom Penh da tashar jiragen ruwa ta Sihanoukville a kasar Cambodiya. Lalle ayyukan raya ababen more rayuwar jama’a karkashin inuwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, sun kyautata hadewar sassa daban daban a Asiya da yankin tekun Pasifik.

Kasar Sin za ta ci gaba da daukar hakikanin matakai don nuna yadda take aza harsashi a Asiya da yankin tekun Pasifik, da raya yankin da kuma kawo alheri ga yankin. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Zamantakewar Aure Tsakanin Miji Da Mata: Wa Aka Fi Zalunta?

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.