A wani gaggarumar ci gaba da aka samu a tafiyar darikar Tijjaniya, Khalifa Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Inyass ya sanar da wasu sauye-sauye domin karfafa zumunci da hadin kai na darikar a fadin duniya baki daya, an bayyana haka ne a sanarwar da Khalifan ya fitar bayan tattaunawa tare da manyan masu ruwa da tsaki da manyan Shehunai.
Shawarar ta biyo bayan kammala bikin mauludin da aka yi na kwanan nan inda aka samu halartar ‘yan darikar Tijjaniyyah daga ko’ina a fadin duniya. Khalifa ya taya al’ummar Musulmai murnar wadannan bukukuwan da aka yi, ya kuma bukaci karin hadin kai a tsakanin al’umma da karin riko da koyarwar addinin Musulunci.
Manyan shawarwarin da akia cimma sun hada da:
Dakatar da Ofishin Khalifan Tijjaniya A Nijeriya
A wata shawara mai cike da tarihi, an dakatar da tafiyar da ofishin Khalifan Tijjaniyyah a Nijeriya. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, haka na tattare da komawar Khalifa Muhammad Sanusi II kan karagar sarautar Kano. Sheikh Mahy ya ce, an yanke wannan shawarar ce domin saukaka tafiyar da shugabanci a tsakanin ‘yan darikar Tijjaniyyah a fadin Nijeriya.
Manyan Shehunan Tijjaniyyah Za Su Ci Gaba da Tafiyar Da Al’amurra
A halin yanzu manyan Shaihunai biyu na Darikar Tijjaniyyah a Nijeriya, Sheikh Tahir Usman Bauchi da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Husaini ne za su ci gaba da kula da al’amurra. “Iliminsu, basirarsu da tsayuwarsu zai taimaka wajen jagorantar mabiya darika a Nijeriya kamar yadda suka yi a shekarun da suka gabata,” in ji Khalifah.
Shugabancin Kwamitin Maulud Na Kasa
A halin yanzu, gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse na Nijeriya zai zama karkashin jagorancin Sheikh Mahy Niasse kai tsaye tare da hadin gwiwar sauran Shehunai da Mukaddamai domin tabbatar da nasarar gudanar da bikin Mauludin wanda ya zama wata kafa ta hadin kan mabiya Darikar Tijjaniyyah a fadin duniya.
Kafa Majalisar Darikar Tijjaniyyah Ta Duniya
A wani mataki na tabbatar da hadin kai na ‘yan Tijjaniyah a fadin duniya, an kafa ofishi na kasa da kasa da zai kula da yadda za mu yi nasarar kafa majalisar Darikar Tijjaniyah ta Duniya ‘World Tijjaniyyah Assembly’. Ta wannan ofishin da za a kafa majalisar, wannan majalisar za ta zama kafar karfafa hadin kai da aiki tare a tsakanin Shehunan Darikar Tijjaniyyah a fadin duniya da sauran mabiya akidoji daban-daban.
Wadannan shawarwarin sun zama wani sabon shafi ga ‘yan darikar Tijjaniyyah a fadin duniya. “Khalifa Sheikh Mahy Sheikh Ibrahim Niasse ya nemi dukakn ‘yan darika su hada kansu domin tabbatar da samun nasarar da aka sa a gaba. Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba mu ikon aiwatar da wannan shawarwarin domin amfanar ‘yan darikar Tijjaniyyah da al’umma gaba daya,” in ji sanarwar.
Martanin ‘Yan Tijjaniyyah
An samu amincewa da murna a kan wadannan shawarwarin daga ‘yan darikar Tijjaniyyah a fadin Nijeriya. A tattaunawarsa da wannan jaridar, wani dan Tijjaniyyah daga Kano, Mallam Musa Bello, ya nuna jin dadinsa a kan shwarwarin: “Wannnan muhimman al’amura ne gare mu. Sheikh Tahir Usman Bauchi da Sheikh Shariff Saleh za su samar mana da jagorancin da ya kamata. Za kuma mu ci gaba da kasancewa tare da shugabancin Khalifa Niasse, musamman ganin yadda yake karfafa ‘yan Tijjaniyyah.”
Haka kum, sanannen malamin addnin musuluncin nan, Dakta Abdullahi Ahmad ya nuna jin dadinsa, musamman yadda ake shirin kafa ofishi na kasa da kasa “Wannan wani hangen nesa ne da zai karfafa ‘yan Tijjaniyyah tare da samar musu da murya daya a fadin duniya.”