• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Mara Wa Takarar Atiku Abubakar Baya

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Bauchi

Babban Malamin Darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ayyana goyon bayan takarar Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a zaben da za a fafata a ranar Asabar.

Sheikh Dahiru ce, zabin Atiku tamkar neman canji ne da halin da al’ummar kasar nan suka samu kansu a karkashin gwamnatin da ke ciki wato APC.

  • ‘Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban APGA Har Lahira A Ebonyi
  • Tsarin MIDAS Ya Kawo Sauyin Yadda Ake Kula Da Iyakoki —Jere

Atiku dai shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP wanda ke neman kujerar tare da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, hadi da Peter Obi na LP gami da sauran.

A wani sakon sautin murya na ‘yan dakika da Shehin ya fitar da kuma wakilinmu ya tabbatar da ingancinsa daga hadiman Shehin, Sheikh ya ce, bai dace a cuci mumini har sau biyu a rami daya ba, don haka ne suke naman canji a kasar nan.

A sakon da ya aike wa ‘yan kasa na cewa: “Allah ya kawo mu lokacin zabe, jama’an kasa ‘yan uwana ‘yan Nijeriya. Annabi (S) yana cewa, bai kamata a ciji mumuni sau biyu a rami daya ba. Abu ya cijeka a wannan ramin to ya kamata ka dauki hannunka ka sanya a wani ramin kuma.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

“Sabo da haka na ji wadansu mutane su na cewa a zabi wanda za a zaba ya daura mana a kan inda muka tsaya; to ai inda muka tsayan ba dadi muka ji balle mu daura a kai. Mutum sai ya ji dadi yake cewa a kara a mini, in bai ji dadi ba baya cewa a kara mini.

“Saboda haka ina wa’azi ina kira ina bada shawara a zabi inda za a samu canji ko Allah zai canza mana. Inda muka tsaya ba mu ji dadi ba balle a daura mana a kai.”

Dahiru Bauchi, ya ce, mutanensa sun fitar da Atiku a matsayin dan takararsu, don haka shi ma ya mara musu baya, “Mutane na sun bada shawarar cewa su Atiku za su zaba, ni kuma ba zan rabu da mutane ne ba. Zan nanata mutane ne da suke yin siyasa sun ce Atiku za su zaba tun da ga wanda za su zaba ba zan rabu da su ba ina tare da su. Allah ya zaba mana alkairi.”

Ya yi addu’ar cewa Allah sa a yi zaben lafiya a kammala lafiya kuma Allah sa a zabi shugabanni na kwarai da za su taimaki kasar nan, “Allah sa a samu shugaban da zai ji tausayin talakawa ba kamar yadda muka fito ba.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

sallah
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
Next Post
APC Ta Soki Sabon AIG Da Kwamishinonin ‘Yansanda 4 Kan Ziyartar Wike

APC Ta Soki Sabon AIG Da Kwamishinonin 'Yansanda 4 Kan Ziyartar Wike

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

October 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

October 15, 2025
An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

October 15, 2025
sallah

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025
Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

October 15, 2025
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.