ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sheikh Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa

by Sulaiman
1 year ago
Daurawa

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su guji gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar nan.

Ana shirin gudanar da zanga-zangar na kwanaki 10 domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta sakamakon hauhawar farashin man fetur, hauhawar farashin kayayyakin abinci, rashin tsaro da dai sauransu.

  • Ma’aikatan Ruwa Na Jihar Kaduna Sun Yi Zanga-zangar Rashin Albashi
  • Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta

Amma a hudubar da Sheikh Daurawa ya gabatar a Kano a Juma’ar da ta gabata, ya yi nuni da cewa zanga-zangar tana da illa fiye da alherinta, kuma bai kamata a karfafa mata gwiwa ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ba ma goyon bayan zanga-zangar saboda mun ga abin da ya faru a Siriya, Sudan, Libya da Iraki.

“Wataƙila za a gudanar da zanga-zangar ne da kyakkyawan nufi amma wasu masu mugun nufi za su iya shiga ciki su bata lamarin. Dukkanmu mun san da shirin masu tayar da kayar baya na kasa da suke shiri don raba kasa. Suna da kudi da makamai. Za su yi amfani da ku a cikin wannan zanga-zangar don cimma burinsu,” inji shi.

LABARAI MASU NASABA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ya ba da shawarar cewa, a maimakon yin zanga-zanga, ya kamata a nemi hanyoyin diflomasiyya da suka hada da baiwa gwamnati shawara da masu ruwa da tsaki kan matakan da suka dace don magance matsalar.

“Ba tsoro muke ji ba. Amma zanga-zanga ba ta haifar da sakamako mai kyau. Mutane sukan ƙare da rasa ɗan abin da suke da shi. Ya kamata mu ba gwamnati shawara kan abin da za ta yi maimakon haka. Amma a cikin wannan mawuyacin lokaci, ya kamata mu yi taka tsantsan da abin da muke faɗa ko aikatawa,” in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
Hotuna

HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi

December 20, 2025
Next Post
kotu

Badakalar Kudade Fiye Da Miliyan 37: Kotu A Kebbi Ta Umarce CSP Rano Ya Nemo Shaidun Kare Kansa

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.