A ranar Alhamis jagoran ‘yan uwa Musulmai a Nijeriya da aka fi sani da Shi’a, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya halarci addu’ar kwanaki bakwai na rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Shaikh Dahiru Usman Bauchi tare da miƙa cikakken ta’aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin.
Ta’aziyyar wacce ta gudana a Masallacin marigayin da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi, Ƙani kuma shaƙiƙin Shaikh Zakzaky, Malam Badamasi Yaqoub da babban ɗansa, Muhammad Zakzaky tare da wasu malamai ne suka wakilci Malam Zakzaky.
- Duniya Za Ta Kara Kyau In Ba A Nuna Fin Karfi
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 74, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace 318 A Watan Nuwamba
Da ya ke miƙa ta’aziyya a madadin Shaikh Zakzaky, Malam Badamasi Yaqoub, ya ce duniya ce ta yi rashin babban bango wanda ya hidimta wa addinin Musulunci.
Ya ce: “Muna jaddada gaisuwa ga iyalai, ɗaliban Shehu Dahiru Bauchi, ba ɗaliban ba kawai ba har ma da al’ummar duniya baki ɗaya domin rashin Shehu Dahiru Bauchi kamar rashi ne da duniya ta yi. Domin kamar wani bango ne gaba ɗaya. Mahaddaccin Alkur’ani wanda babu kamar irinsa, wanda ya zo da shigen tafsiri wanda a duniya ba a ga mai tafsiri irinsa ba; wanda ya ke fassara Kur’ani da abin da ke ƙwaƙwalwarsa ba tare da ya duba komai ba.’
Ya ƙara da cewa, dukkanin bayani da fassara tare da hadisai da Shaikh Dahiru ke kwararowa da kai ya ke yinsu ba tare da ya sanya littafi a gabansa ba, ya ce babu kamarsa a duk duniya.
Ya ƙara da nuna irin gudunmawar da marigayin ya bai wa addinin Musulunci, “Ko ka ƙi ko ka so Sheikh Dahiru Bauchi ya taimakeka ko kana ɓangarensa ko ba ka ɓangarensa, Sheikh Dahiru Bauchi Malaminka ne. Domin Malamin Kur’ani ne. Allah ya yi masa rahama.”
“Muna jaddada gaisuwa gareku (iyalai) gaba ɗaya bisa wannan babban rashi. Allah ya masa rahama.”
Ya ce bisa babban rashin da jimamin wannan rashin da aka yi ne ya sana jagoran harƙa musulunci Shaikh Malam Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky ya turo shaƙiƙansa da iyalansa domin su zo su yi wa iyalan Shehu Dahiru Bauchi ta’aziyya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikanshi ya haramsheshi, Allah ya sa ya huta Allah ya kaddara rayuwarshi na lahira ya fi masa na duniya alkairi. Allah sa kabarinsa ya zama rauda fil riyadul Jannah.
Da ya ke amsar ta’aziyyar, Khalifa Shaikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya nuna godiyarsu ga ta’aziyyar, tare da bayyana rashin Shehin a matsayin abin yi ta’aziyya wa juna gaba daya. Ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shaikh Ibraheem Zakzaky da marigayi Shaikh Dahiru Bauchi, inda ya bada misali da irin lokutan da Shaikh Zakzaky ya rika ziyartan Shehi a baya, har Shehi kan gabatar da shi ya ja su Sallah.
“Mun gode da wannan ta’aziyyar, Amma ta’aziyyar namu ne dukka. Shaikh Ibraheem Al-Zakzaky ba bako ba ne a wannan gidan ina ji lokacin da ya ke zuwa ziyara (wajen magariyi) yawanci in ya zo ma Shehi ya na sa shi ya jagorancemu sallah, to Allah ya saka musu da alkairi, Allah ya daukaka addinin musulunci.
Khalifan Shehin ya yi adduar Allah ya ɗauka musulunci da musulmai ya ƙara haɗa kan al’ummar ƙasar nan baki daya.
Idan za a tuna dai Shaikh Dahiru ya rasu ne da safiyar ranar Alhamis inda ya ke cika kwanaki bakwai da rasuwar. An gudanar da addu’o’i na musamman da nufin Allah ya gafarta wa mamacin. Ɓangarori daban-daban ne suke ci gaba da ta’aziyyarsu.














